Shiri Ya Baci: Sanatan PDP Ya Fice daga Jam'iyyar a Bauchi
- Jam'iyyar PDP ta rasa daya daga cikin sanatocinta wanda yake wakiltar mazabar Bauchi ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya
- Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya bayyana cewa daga cikin dalilansa na ficewa daga jam'iyyar har da rikice-rikicen da suka addabe ta
- Ya bayyana cewa rikice-rikicen sun hana shi sakewa wajen gudanar da wakilcin da ya je yi a majalisar dattawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Sanata Samaila Dahuwa Kaila, wanda ke wakiltar mazabar Bauchi ta Arewa, ya fice daga jam'iyyar PDP.
Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya danganta matakinsa na ficewa daga PDP da rikice-rikicen cikin gida da suka ki karewa a jam’iyyar.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta ce Sanata Samaila Dahuwa wanda bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga ba, ya sanar da murabus dinsa ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 6 ga watan Oktoba, 2025.
Sanata Samaila Dahuwa ya yi murabus daga PDP
An aika da wasikar zuwa ga shugaban jam'iyyar PDP na mazabar Tsakuwa/Kofar Gabar, a karamar hukumar Katagum ta jihar Bauchi.
A cikin wasikar, Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka raba jam’iyyar gida biyu sun takura masa wajen gudanar da aikinsa na majalisa yadda ya kamata.
Ya ce bayan tattaunawa da abokan siyasa da magoya bayansa, ya yanke shawarar canja jam'iyyar siyasa, jaridar Leadership ta kawo labarin.
“Rikice-rikicen cikin gida da suka haddasa rarrabuwar kawuna a cikin PDP suna shafar yadda nake gudanar da aikina na wakilci a majalisar dattawa ta 10."
“Saboda haka, ina rubuto wannan wasika domin sanar da ku cewa daga yau na fice daga jam’iyyar PDP."
- Sanata Samaila Dahuwa Kaila

Source: Facebook
Sanata Dahuwa ya godewa jam'iyyar PDP
Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya godewa jam’iyyar saboda damar da ta ba shi, tare da fatan za a ci gaba da huldar siyasa a nan gaba domin ci gaban kasa.
A halin yanzu, bai bayyana jam’iyyar da zai shiga ba, kuma kokarin da manema labarai suka yi don samun karin bayani daga gare shi ta waya bai yi yiwu ba domin bai ɗauki kiran ba.
Karanta wasu labaran kan PDP
- PDP za ta rushe: Gwamna, 'yan majalisa 24 da kansiloli 260 za su koma APC
- Gwamna na shirin komawa APC, tsohon jagora a Majalisar Dattawa ya fice daga PDP
- Ya bar PDP? Gaskiya ta fito game da 'sauya sheƙar' tsohon gwamnan Benue zuwa APC
Tsohon sanata ya fice daga jam'iyyar PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Edo ta Kudu a majalisar dattawa, Ehigie Uzamera, ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar PDP.
Tsohon sanatan ya sanar da ficewarsa daga PDP ne a cikin wasikar da ya aikewa shugaban jam'iyyar na Ward 12, karamar hukumar Ovia ta Arewa, Mr. Osaigbovo Godspower.
Ehigie Uzamera ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda neman wata jam'iyyar da za ta ba shi damar ci gaba da hidimtawa jama'arsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

