Jam'iyyar LP Ta Mika Bukata ga Atiku, Ta Tabo Batun Janyewar Peter Obi a 2027

Jam'iyyar LP Ta Mika Bukata ga Atiku, Ta Tabo Batun Janyewar Peter Obi a 2027

  • Jam'iyyar LP ta mika kokon bararta ga tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar
  • LP ta bukaci Atiku ya hakura da burinsa na yin takara don marawa Peter Obi baya a zaben shugaban kasa na 2027
  • Hakazalika ta bayyana matsayarta kan batun cewa tsohon 'dan takaran zai hakura da neman mulkin kasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar LP ta karyata jita-jitar da ke cewa dan takararta na shugaban kasa a 2023, Peter Obi, zai iya janyewa wani ɗan takara a zaben 2027

Jam'iyyar LP mai hamayya ta nuna cewa yin haka zai zama cin amanar miliyoyin ‘yan Najeriya da ke neman sauyi.

LP ta ba Atiku Abubakar shawara
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi. Hoto: @PeterObi, @atiku
Source: Facebook

LP ta ce Peter Obi ba zai janyewa kowa ba

Mai rikon mukamin sakataren yaɗa labarai na kasa na LP, Tony Akeni, ya bayyana hakan yayin wata hira da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa da aka ja kunnensu kan yin takara a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a martaninsa kan tattaunawar da ke gudana game da yiwuwar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa kafin babban zaɓen 2027.

Tony Akeni ya ce janyewar Peter Obi daga takara daidai yake da kwace kashi 90 cikin 100 na fatan ‘yan Najeriya wajen samun ceto daga sabuwar gwamnati.

"Tilasta wa Peter Obi ya janye daga takara daidai yake da ɗauke kashi 90 cikin 100 na fatan ‘yan Najeriya na samun ceto daga sabuwar gwamnati."
“Ina ganin lokaci zai zo da za mu haɗa kai, mu masu ruwa da tsaki mu ɗauki sahihin mataki a lokacin da ya dace. Amma wannan lokacin bai yi ba tukuna, zai zo ne kusa da lokacin zaben fidda gwani."

- Tony Akeni

Ya tabbatar da cewa Peter Obi ko 'yan kungiyar Obidient ba za su janye daga takarar shugaban kasa ba.

"Idan haɗakar jam’iyyun adawa ba su ɗauki sahihin mataki ba, to mu dai muna kan gaba wajen neman shugabancin kasa.”

Kara karanta wannan

'Mu fa sai Jonathan,' : Kungiyar Arewa ta dage tsohon shugaban kasa ya sake takara

- Tony Akeni

Wace bukata LP ta neman wajen Atiku?

Tony Akeni ya kuma roki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da ya nuna kaunarsa ga kasar nan ta hanyar yin abin da ya dace, ya ba Peter Obi dama a 2027.

LP ta bukaci Atiku ya hakura da yin takara
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: @atiku
Source: Facebook
“Ya kamata Atiku ya yi tunani kan tarihin da zai bari. Shin yana so a tuna da shi a matsayin mutumin da ya sadaukar da Najeriya saboda burinsa amma bai cin ma shi ba?"
"Ko a matsayin wanda ya sadaukar da burinsa saboda Najeriya, ya ceto ta daga kalubale ya mayar da ita kan hanyar ci gaba?"

Tony Akeni ya bayyana cewa haɗakar “AGOBI’27” (Atiku Give Us Obi 2027) ta samo asali ne daga wasu masu ruwa da tsaki da ke kokarin tausasa zuciyar Atiku domin ya goyi bayan takarar Peter Obi a matsayin zaɓin ‘yan adawa.

Atiku ya bukaci a binciki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci a binciki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

Atiku ya bukaci a kafa kwamitin da zai binciki takardun karatun Shugaba Tinubu da na sauran ministocinsa.

Ya bayyana cewa murabus ɗin Uche Nnaji daga mukamin Ministan kimiyya da fasaha yunƙurin ɓoye abin kunya ne da ke cikin gwamnatin Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng