Zaben Ekiti: Gwamna Ya Tsallake da APC Ta Hana Manyan 'Yan Siyasa 2 Shiga Takara
- Kwamitin tantance wadanda suka nuna sha'awar neman takara a zaben fitar da gwanin jam'iyyar APC a jihar Ekiti ya gama aikinsa
- Jam'iyyar APC ta bayyana cewa Gwamna Biodun Oyebanji, wanda ke neman tazarce a zaben 2026 ya tsallake matakin tantancewa
- Sai dai APC ta hana jiga-jigan yan siyasa biyu, Kayode Ojo da Abimbola Olawumi shiga zaben tsaida gwanin saboda rashin cika sharudda da ka'idoji
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ekiti - Jam’iyyar APC mai mulki ta hana manyan 'yan siyasa biyu, Kayode Ojo da Abimbola Olawumi shiga zaɓen fidda dan takarar gwamnan jihar Ekiti.
Jam'iyyar ta bayyana cewa Mista Ojo da Olawumi ba su cancanci tsayawa takara karkashin inuwar APC a zaben gwamnan Ekiti da ke tafe ba.

Source: Twitter
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da APC ta fitar bayan taron kwamitin gudanarwa (NWC) na kasa karo na 179 wanda aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, cewar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta tantance Gwamna Oyebanji a Ekiti
A cikin sanarwar, APC ta tabbatar da cewa gwamnan Ekiti mai ci, Biodun Oyebanji, ya samu sahalewar jam’iyyar don yin takara karo na biyu.
Mataimakin sakataren yaɗa labarai na APC ta a lasa, Durosinmi Meseko, ya bayyana cewa kwamitin NWC ya duba kuma ya amince da rahoton kwamiti tantance ‘yan takarar gwamnan jihar Ekiti.
Mista Meseko ya ƙara da cewa Atinuke Omolayo ta samu amincewar jam’iyyar don yin takara a zaben fidda gwanin da za a shirya.
Me yasa APC ta hana mutum 2 takara a Ekiti?
Mataimakin kakakin APC ya bayyana cewa an gudanar da tsarin tantancewar ne bisa dokokin jam’iyyar da ƙa’idar gudanar da zaɓen fidda gwani, tare da tabbatar da gaskiya da adalci.
Sai dai kuma bai bayyana dalilan da suka sa aka ƙi amincewa Ojo da Olawumi su fafata a zaben fidda gwanin APC, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
'Mu fa sai Jonathan,' : Kungiyar Arewa ta dage tsohon shugaban kasa ya sake takara
Durosinmi Meseko ya ce ‘yan takarar da suka samu amincewa yanzu za su shiga mataki na gaba na tsarin fidda ɗan takarar gwamna.

Source: Twitter
Yaushe za a gudanar da zaben gwamnan Ekiti?
Idan ba ku manta ba, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta tsara gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ekiti a ranar 20 ga Yuni, 2026.
Gwamna Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC na kokarin neman tazarce zuwa zango na biyu, amma yana fuskantar kalubale masu yawa daga cikin gida da kuma yan adawa.
Gwamnan Ekiti ya kori kwamishinoni da hadimai
A wani labarin na daban, kun ji cewa a daidai lokacin da ake tunkarar zabe a Ekiti, Gwamna Biodun Oyebanji ya kori wasu kwamishinoni da jami'an gwamnatinsa.
An umarci kwamishinoni da manyan masu ba da shawara na musamman da abin ya shafa, su mika mulki ga babban sakatare ko kuma ma’aikacin gwamnati mafi girma a mukami a ma'aikatar da suke.
Gwamna Oyebanji ya gode wa mambobin majalisar zartarwa da suka kammala wa’adinsu tare da yi musu fatan alheri a ayyukan da za su gudanar a nan gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
