'Mu fa sai Jonathan,' : Kungiyar Arewa Ta Dage Tsohon Shugaban Kasa Ya Sake Takara
- Wata ƙungiyar a Arewacin Najeriya ta bayyana wanda take goyon baya a zaben shekarar 2027 da ke tafe
- Kungiyar da ke marawa PDP baya ta ce babu ja da baya kan marawa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan baya a zaben 2027
- Ta yaba da jagorancin Umar Damagum, tana mai cewa lokaci ya yi da ‘yan jam’iyyar za su haɗa kai domin dawo da mulki hannun PDP
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kebbi - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan na ci gaba da samun goyon bayan kan takara a 2027.
Ƙungiyar da ke goyon bayan Jam’iyyar PDP a Arewa ta bayyana cewa babu ja da baya kan marawa tsohon shugaban ƙasa baya.

Source: Twitter
Jonathan ya samu kwarin guiwar takarar 2027
Rahoton Vanguard ya ce kungiyar ta ce za ta goyi bayansa ne domin tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
Wannan sanarwar ta fito ne bayan taronsu na takwas da aka gudanar a Birnin Kebbi daga ranar 8 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025.
Kungiyar ta ce babu shakka Goodluck Jonathan ne mutum mafi dacewa da zai gyara sunan jam’iyyar, tana mai cewa batun cancanta ya riga ya samu.
Sun bayyana Jonathan a matsayin mutum mai son zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba, wanda ya sadaukar da kansa don zaman lafiyar ƙasa lokacin da ya mika mulki cikin lumana a 2015.
Shugaban PDP ya samu goyon bayan 'yan jam'iyya
Ƙungiyar ta bayyana goyon bayanta ga mukaddashin shugaban jam’iyyar, Ambasada Iliya Umar Damagum.
Ta ce Damagum yana jagorantar sake gina jam’iyyar ta hanyar karfafa haɗin kai da ladabi tsakanin mambobinta a faɗin ƙasar nan.
A cewar ƙungiyar, lokaci ya yi da ‘yan jam’iyyar za su haɗa kai domin tabbatar da dawowar PDP kan mulki a 2027.

Source: Twitter
Korafi kan wasu shugabannin PDP a Najeriya
Sai dai ƙungiyar ta nuna damuwa kan wasu shugabannin jam’iyyar da ke cin moriyar gwamnati mai ci, tana zargin wasu daga cikin NWC suna aiki da APC.
Ta ce irin wannan ba zai taimaka ba wajen farfaɗo da jam’iyyar, saboda haka dole ne a ɗauki mataki mai tsauri, cewar rahoton Punch.
Haka kuma, ƙungiyar ta zargi ministan Abuja Nyesom Wike da haddasa rarrabuwar kawuna a jam’iyyar PDP, tana cewa ya zama dole a dakatar da tasirinsa kafin ya lalata jam’iyyar.
A ƙarshe, ƙungiyar ta jaddada amincinta ga shugabancin PDP tare da alƙawarin ci gaba da aiki tukuru don kafa ingantacciyar jam’iyya mai haɗin kai wacce za ta karɓi mulki a 2027.
An shawarci Jonathan kan takara a 2027
Kun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Lagos, Abdul-Azeez Adeniran, ya ja kunnen tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan
Dattawan Arewa sun bayyana matsayarsu kan zaben 2027, ta fadi kalan dan takararta
Kusa a APC ya bukaci Jonathan da ka da ya yi kuskuren yin takara da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Adeniran ya bayyana cewa babu wani dan siyasa da zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
