Sanatan APC Ya Kafa Misali da Trump, Ya Ce da Yiwuwar Ya Zama Shugaban Najeriya a 2039
- Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa da yiwuwar ya nemi kujerar shugaban kasa a 2039 bayan Arewa ta kammala wa'adin shekaru takwas
- Kalu, Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa ya ce yana da gogewa da kuma kwarewar da ake bukata wajen jagorantar Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Abia ya kafa misali da Shugaba Donald Trump na Amurka yayin da aka tuna masa da batun shekarunsa a 2039
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa ba laifi ba ne idan ya nemi zama shugaban ƙasa a lokacin yana dan shekara 78.
Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa ya ba da misali da shugaban Amurka, Donald Trump, yana mai cewa zai iya neman shugabancin Najeriya a 2039.

Kara karanta wannan
'Mu fa sai Jonathan,' : Kungiyar Arewa ta dage tsohon shugaban kasa ya sake takara

Source: Facebook
Kalu ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television, a shirin Politics Today ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Kalu na zon zama shugaban Najeriya
Ya sake jaddada cewa yana da ƙwarewa, nagarta da gogewa da za su iya ba shi damar jagorantar Najeriya.
"Har yanzu ina da buri kuma ina da ƙwarewa da cancanta na zama shugaban ƙasa. Amma ba a 2027 ba, yanzu ina goyon bayan Shugaba Tinubu,” in ji Kalu.
Mai gabatar da shirin ya tunatar da shi cewa yanzu shekarunsa 65 yanzu, kuma idan ya jira tsawon shekara 12 lokacin da mulki zai koma Kudu, ya kai shakara 78 kenan.
Orji Kalu ya kafa misali da Shugaba Trump
Sanata Kalu ya ba shi amsa da cewa shekaru ba matsala ba ne gare shi, ya ce:
“Me ya sa ba zai yiwu ba? Shugaba Trump yana da shekaru 79. Idan ina da lafiya kuma Allah ya ba ni rai da ƙoshin lafiya, shekaru ba matsala ba ne.

Kara karanta wannan
"Tsohon shugaban kasa ya yi karya," Sanata Kalu ya tona abin da ya faru a kafin zaben 2007
"Abin da ke cikin kwakwalwata shi zan bayar. Ba shekaru ke da muhimmanci ba, cancanta ce da shirye-shirye."
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana kansa a matsayin jagoran siyasar yankin Kudu maso Gabas, yana mai cewa ya shiga gaban tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.
Sai dai Kalu ya ƙi tsunduma sosai cikin batun Peter Obi, inda ya ce zai yi haka ne kawai idan za a shirya tattaunawa kai tsaye tsakaninsu, in ji rahoton Tribune Nigeria.

Source: Facebook
'Dan Majalisar Dattawa ya nanata cewa ya cancanci zama shugaban Najeriya, amma a zaben 2027, zai goyi bayan tazarcen Bola Ahmed Tinubu.
Kalu ya fadi abin da ya faru kafin 2007
A baya, kun ji cewa Sanata Orji Kalu ya zargi tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo da yin ƙarya kan ikirarin cewa bai nemi wa’adi na uku ba bayan karewar wa'adin mulkinsa.
Kalu ya ce Obasanjo da kansa ya kira shi har cikin fadar shugaban ƙasa lokacin yana matsayin gwamnan Abia, ya shaida masa cewa yana da niyyar ƙara wa’adi ko da daya ne.
A cewarsa, tun da ya sa kafa ya shure wannan kudiri na Obasanjo, suka samu sabani a tsakaninsu har zuwa karshen wa'adin mulkinsu gaba daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
