"Tsohon Shugaban Kasa Ya Yi Karya," Sanata Kalu Ya Tona Abin da Ya Faru a kafin Zaben 2007

"Tsohon Shugaban Kasa Ya Yi Karya," Sanata Kalu Ya Tona Abin da Ya Faru a kafin Zaben 2007

  • A watan Satumba da ya shige, tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya musanta labarin cewa ya so neman zango na uku a 2027
  • Sanata Orji Uzor Kalu, wanda ke matsayin gwamnan jihar Abia a wancan lokacin, ya ce Obasanjo karya ya yi domin ya nemi ci gaba da mulki
  • Kalu ya bayyana yadda Obasanjo ya kira shi har fadar shugaban kasa kuma ya fada masa shirinsa na neman wa'adi na uku bayan 2007

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata Orji Uzor Kalu, mai wakiltar Abia Arewa a majalisar dattawa, ya zargi tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da yin ƙarya kan ikirarin cewa bai nemi wa’adi na uku ba a mulkinsa.

Kalu ya ce Obasanjo da kansa ya kira shi fadar shugaban ƙasa lokacin yana mulki, ya shaida masa cewa yana da niyyar ƙara wa’adi ta hanyar gyaran kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya kafa misali da Trump, ya ce da yiwuwar ya zama shugaban Najeriya a 2039

Sanata Orji Kalu.
Hoton Sanata Orji Kalu a wurin hira da manema labarai. Hoto: Orji Uzor Kalu
Source: Twitter

Sanata Kalu ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da tashar Channels tv ranar Laraba, 8 ga watan Oktoba, 2025.

Abin da Obasanjo ya ce kan wa'adi na 3

Tun farko dai Obasanjo ya fito ya karyata labaran da ake yadawa cewa ya nemi zarcewa zuwa zango na uku bayan karewar wa'adin mulkinsa a 2007.

Da yake jawabi a wani taro da ya halarta a Ghana, Obasanjo ya ce:

“Babu wani ɗan Najeriya da ya mutu ko wanda yake raye da zai ce na kira shi na ce ina son wa’adi na uku. Ba wawa ba ne ni. Da ina so, na san yadda zan yi.”

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yayin da yake martani kan haka, Sanata Kalu ya karyata wannan magana ta Obasanjo.

Sanata Orji Kalu ya karyata Obasanjo

Tsohon gwamnan jihar Abia ya ce:

“Cikin girmamawa, abin da Obasanjo ya faɗa a Ghana ƙarya ce tsantsa. Galibin mutanen da suka san abin da ya faru suna nan raye, David Mark yana nan, sauran ma su na nan kuma sun san gaskiya.

Kara karanta wannan

Najeriya ta karyata bankin duniya kan samun talakawa miliyan 139 a mulkin Tinubu

Sanata Kalu ya ce Obasanjo ne ya gayyace shi zuwa fadar shugaban ƙasa domin tattaunawa kan yadda za a yi gyaran kundin tsarin mulki da zai ba shi damar sake tsayawa takara.

Orji Kalu ya yi bayanin abin da ya faru

“Ya gayyace ni zuwa Aso Rock, ya gaya mani game da batun wa’adi na uku. Sanata Uche Chukwumerije ya kawo Naira miliyan 50 don a raba, suka tambaye ni ko zan karɓa a matsayina na gwamna, na ce a’a, bana so.
"Shi ma mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (Nuhu Ribadu) ya san Obasanjo ƙarya yake, domin ya san duk abin da ya faru a wancan lokacin."

- Orji Uzor Kalu.

Sanata Orji Kalu.
Hoton Sanata Orji Kalu da na tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo. Hoto: Orji Uzor Kalu
Source: Facebook

Ya ce rikicinsa da Obasanjo ya fara ne bayan ya ƙi goyon bayan wannan shirin, Kuma ya sanar da wasu shugabannin ƙasashen duniya game da abin da ake shirin yi a Najeriya.

Sanata Kalu ya hangi nasarar Tinubu a 2027

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa yana ganin lallai Bola Tinubu zai samu nasara a karo na biyu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar da Peter Obi da za su iya kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

Sanata Kalu ya kara da cewa duba da abubuwan da Tinubu ya yi kawo yanzu, ba ya tunanin 'yan Najeriya za su juya masa baya a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262