'Jonathan, Atiku da Peter Obi ba Za Su Iya Doke Shugaba Tinubu a Zaben 2027 ba'

'Jonathan, Atiku da Peter Obi ba Za Su Iya Doke Shugaba Tinubu a Zaben 2027 ba'

  • Orji Uzor Kalu mai wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa ya ce har yanzu bai ga dan siyasar da zai iya doke Tinubu a 2027 ba
  • Sanata Kalu, tsohon gwamnan Abia ya yi ikirarin cewa Jonathan, Atiku da Peter Obi ba za su iya samun galaba kan Shugaba Tinubu ba
  • 'Dan Majalisar Dattawan ya kuma gargadi Jonathan kan rade-radin da ake na zai fito takara, yana mai cewa doka ta haramta masa hakan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Sanata Orji Kalu, ya bayyana cewa ba shi da tantamar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi tazarce a babban zaben 2027.

Sanata Kalu, dan Majalisa mai wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa ya nuna kwarin gwiwar cewa Tinubu zai iya doke duka manyan yan adawar da ke burin fitowa takara a zabe na gaba.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Tsohon shugaban kasa zai gana da Tinubu kan jagoran 'yan ta'adda a Najeriya

Sanata Orji Uzor Kalu.
Hoton Sanata Orji Kalu a ofishinsa na Majalisar Dattawa. Hoto: Orji Uzor Kalu
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels yau Laraba, 8 ga watan Oktoba, 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalu ya nuna kwarin gwiwa kan Tinubu

Ya ce tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon dan takarar LP a zaben 2027, Peter Obi, ba za su iya doke Tinubu ba.

Kalu ya ce:

"Babu daya daga cikin wadannan mutanen da ke kokarin tsayawa takara da zai iya kayar da Shugaba Tinubu. Mun san kanmu, dukkanmu mun san kanmu, me za su kawo wa 'yan Najerda da mu kawo shi ba?"

Jonathan, Atiku da Obi za su iya doke Tinubu?

Da aka tambaye shi ko Jonathan da Atiku da Obi na cikin ‘yan siyasar da ya yi magana a kai, sai ya ce “Duk abin da ka kira su, babu daya daga cikinsu da zai iya kayar da Tinubu.”

Kara karanta wannan

Malami ya yi hasashen mai nasara a zaben 2027, ya ce gwamna zai taka wa Tinubu birki

A cewar jigon jam’iyyar APC ɗin, Shugaba Tinubu ya taka rawar gani wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa tun da ya karbi ragamar mulkin Najeriya.

Sanata Kalu ya kara da cewa duba da abubuwan da Tinubu ya yi kawo yanzu, ba ya tunanin 'yan Najeriya za su juya masa baya a zaben 2027, cewar rahoton Vanguard.

2027: Sanata Kalu ya gargadi Jonathan

Haka kuma, ɗan siyasar na jihar Abia ya gargaɗi Tsohon Shugaba Jonathan kan sake neman takara a zabe mai zuwa, yana mai cewa doka ta haramta masa yin hakan.

"Da ni ne Shugaba Jonathan, ba zan yi tunanin tsayawa takara ba, domin dokar kasa ta haramta masa, babu wanda zai iya yin fiye da shekaru takwas a kan mulki.
"Idan ni Goodluck Jonathan ne, zan koma gefe ne na ci gaba da zama dattijon kasa kawai," in ji Sanata Kalu.
Jagororin adawar Najeriya.
Hoton tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, Peter Obi da Atiku Abubakar. Hoto: Goodluck Jonathan, Peter Obi, @Atiku
Source: UGC

Sai dai wani matashin dan siyasa, Kwamared Sulaiman Yahaya ya shaida wa Legit Hausa cewa zaben 2027 zai kayatar domin da alamu zai na wasu mamaki.

A cewarsa, babu wani dan siyasa da zai zauna ya fadi wanda yan Najeriya za su zaba, sai dai kawai ya fadi ra'ayinsa ko gwaninsa.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya kafa misali da Trump, ya ce da yiwuwar ya zama shugaban Najeriya a 2039

"Wuka da nama na hannun yan Najeriya, su ne za su yanke wanda za su zaba, maganar Jonathan, Obi da Atiku ba za su iya da Tinubu ba yana hannun kasu kada kuri'a.
"Amma ga dukkan alamu, zaben 2027 zai kayatar matuka, ina hasashen fafatawar za ta yi zafi fiye da zaben 2023," in ji shi.

Sanata Kalu ya ce zai iya mulkin Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa ya cancanci zama shugaban kasa a 2027.

Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia ya ce a shirye yake ya nemi takara a 2027 idan Bola Tinubu ya haƙura da tazarce.

Ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na iya bakin ƙoƙarinsa wajen dawo da komai kan hanya ta yadda kowane dan Najeriya zai amfana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262