Rigimar 'Yan Adawa Ta Kori Sanata, Ya Sanar da Komawa APC a Majalisar Dattawa

Rigimar 'Yan Adawa Ta Kori Sanata, Ya Sanar da Komawa APC a Majalisar Dattawa

  • Sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas, Kelvin Chukwu ya tabbatar da sauya shekarsa hukumance daga LP zuwa APC mai mulki
  • Hakan na kunshe ne a wasikar da ya mikawa Majalisar Dattawa kuma Sanata Godswill Akpabio ya karanta a zaman yau Laraba
  • Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Bamidele ya ce APC na kara karbuwa a fadin kasa ne saboda salon mulkinta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Adadin Sanatocin jam’iyyar APC a Majalisar Dattawa ya karu zuwa 73, bayan sauya sheƙar da Sanata Kelvin Chukwu ya yi daga jam’iyyar LP.

Sanata Chukwu ya tabbatar da sauya sheka daga LP zuwa APC a hukumance ranar Laraba, 8 ga watan Oktoba, 2025.

Sanata Kelvin Chukwu.
Hoton Sanata Kelvin Chukwu, wanda ya bar LP zuwa APC. Hoto: Kelvin Chukwu
Source: Facebook

Majalisar Dattawa ce ta sanar da hakan a zamanta na yau, wanda hakan ya kawo sabon sauyi a Majalisar Dokoki ta 10, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Jonathan, Atiku da Peter Obi ba za su iya doke Shugaba Tinubu a zaben 2027 ba'

Abin da ya kori Sanata Chukwu daga LP

Sanatan, wanda ke wakiltar mazabar Enugu ta Gabas, ya ce ya sauya sheƙa ne saboda abin da ya kira rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar LP.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasikar sauya shekar Sanata Kelvin Chukwu ga sauran abokan aikinsa.

A jawabinsa, Akpabio ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su sake tsara kansu domin samar da dama da dandali mai nagarta wanda zai kara ƙarfafa dimokuraɗiyya a ƙasar.

Akpabio ya roki yan adawa su sasanta kansu

Ya yi gargadin cewa halin da suke ciki na rikice-rikice na iya zama barazana ga ci gaban dimokuraɗiyya a Najeriya, in ji rahoton jaridar Vanguard.

Sanata Akpabio ya ce:

“Ina son a samu jam’iyyar adawa mai ƙarfi a Najeriya, amma idan suna cikin irin wadannan rikice-rikice, me za mu iya yi? Don Allah, ku gyara gidanku. Wannan ne ya sa INEC ke ci gaba da rajistar ƙarin jam’iyyun siyasa.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta rantsar da sababbin sanatoci daga jihohi 2, an jero sunayensu

Me yasa APC ke samun karuwa a Majalisa?

A nasa tsokacin, shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce APC na samun karuwa ne saboda yadda take tafiyar da akalar tattalin arzikin kasa.

“Wannan canjin da ake samu a Majalisar Dattawa na nuna yanayin da ake ciki fadin ƙasa; gwamnatin APC na aiki.
"Asusun ajiyar kudin kasarmu na karuwa, tattalin arziki ya nuna alamun bunkasa, wanda haka ne nuna kasar mu tana kan hanyar fargadowa," in ji Bamidele.
Zauren Majalisar Dattawa.
Hoton zauren Majalisar Dattawan Najeriya. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Da wannan ci gaba, a halin yanzu APC na da mambobi 73, PDP na da 28, LP na da hudu, yayin da APGA ke da biyu, sai SDP da NNPP da suke da ɗaya-ɗaya a Majalisar Dattawa.

Majalisa ta rantsar da sababbin sanatoci 2

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya jagoranci rantsar da sababbin sanatoci biyu da suka lashe zaben cike gurbi.

Sanatocin da suka karbi rantsuwar kama aikin sun hada da Sanata Joseph Ikpea mai wakiltar Edo ta Tsakiya da Sanata Emmanuel Nwachukwu mai wakiltar Anambra ta Kudu.

Kara karanta wannan

Amupitan: Farfesa daga jami'ar Jos na dab da zama sabon shugaban hukumar INEC

Magatakardar Majalisar Dattawa, Emmanuel Ojo ne ya karanta musu rantsuwar kama aiki da biyayya kuma suka maimaita kamar yadda doka ta tanada.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262