Jam'iyyar ADC Ta Kafa Sharuda 4 kafin ba 'Yan Siyasa Tikitin Takara a 2027

Jam'iyyar ADC Ta Kafa Sharuda 4 kafin ba 'Yan Siyasa Tikitin Takara a 2027

  • Jam’iyyar hadaka ta ADC ta sanar da cewa za ta tsayar da ‘yan takara masu halaye guda huɗu da za su samu karbuwa a zabe mai zuwa
  • Shugaban jam’iyyar, Sanata David Mark, ya ce burin ADC ba kawai samun mulki ba ne, sai dai gina jagoranci na mutunci mai ɗorewa
  • Ana hasashen tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar na iya zama cikin jerin masu neman tikitin jam’iyyar a zaben 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta bayyana muhimman sharuɗɗan da za ta dogara da su wajen tantance ‘yan takarar da za su tsaya mata a babban zaɓen 2027.

Shugaban jam’iyyar, Sanata David Mark, ne ya sanar da hakan a taron kwamitin zartarwa na ƙasa da aka gudanar a Abuja a ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya fi ƙarfinka,' Ɗan takarar gwamna ya gargadi Jonathan kan takarar 2027

Shugabannin ADC yayin wani taro a Abuja
Shugabannin ADC yayin wani taro a Abuja. Hoto: @ADC Vanguard
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa David Mark ya bayyana cewa jam’iyyar za ta zaɓi wadanda suka cika ƙa’idar da ta gindaya ne kawai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharudan takara a ADC a zaben 2027

Jam'iyyar ADC ta ce dole wanda zai mata takara ya kasance yana da halaye guda hudu domin shawo kan jama'ar kasa.

1. Hali na gari

2. Kwarewa

3. Jarumtaka

4. Ladabi

David Mark ya ce:

“Ba za mu tsayar da kowa ba face wanda ya cancanta kuma mai daraja a idon al’umma.”

Ya ƙara da cewa manufar ADC ba kawai lashe zaɓe ba ce, sai dai ta kafa jagoranci mai mutunci wanda zai dawo da amincewar jama’a ga gwamnati da tsarin mulki.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na cikin manyan shugabannin ADC da ake ganin na iya sake neman kujerar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar.

Karin bayani daga shugaban jam'iyyar ADC

A jawabin da ya yi, Mark ya bayyana cewa ADC tana shirin kafa jam’iyya mai ƙarfi wadda ba za ta ta’allaka da mutum ɗaya ba.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji dalilin da ya sa Atiku Abubakar ke jan kafa kan batun takara a 2027

Vanguard ta wallafa cewa shugaban jam'iyyar ya ce:

“Jam’iyyunmu suna shahara ne da sunayen wasu mutane, amma ADC za ta kasance kan dokoki, manufofi, da tsari. Za mu kafa jam’iyyar da za ta ɗore bayanmu.”

Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta tabbatar da bin tsarin dimokuraɗiyya na cikin gida, haɗin kai da gaskiya wajen gudanar da harkokinta.

Atiku da wasu 'yan ADC a Abuja
Atiku da wasu 'yan ADC a Abuja. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Manufar ADC kan gwamnati da siyasa

Shugaban ADC ya ce jam’iyyar za ta tabbatar da raba ikon gudanarwa tsakanin majalisa, kotu da fadar gwamnati, tare da tabbatar da adalci a kotuna.

Ya bayyana cewa ADC za ta bi tafarkin diflomasiyya mai ma’ana a Afirka, wacce za ta mayar da hankali kan haɗin kan nahiyar da bunƙasa kasuwanci.

2027: Tawagar EU ta gana da Atiku

A wani rahoton, kun ji cewa tawagar tarayyar Turai ta EU ta gana da Atiku Abubakar kan zaben Najeriya.

Sun gana ne a birnin tarayya Abuja kan gyaran da ake bukata a yi a Najeriya kafin babban zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sahihancin zaben 2027 da tawagar tarayyar Turai

Rahotanni sun bayyana cewa Atiku Abubakar ya bukaci majalisar dattawa da hukumar INEC su gaggauta gyara dokokin zabe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng