Yadda Shugaban Majalisa Ya Ceto Shugaban Marasa Rinjaye daga Yunkurin Tsige Shi

Yadda Shugaban Majalisa Ya Ceto Shugaban Marasa Rinjaye daga Yunkurin Tsige Shi

  • Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya yi nasarar kawo tsaiko a shirin tsige Shugaban Marasa Rinjaye na majalisa
  • A makon nan ne aka fara shirin tsige Kingsley Chinda daga kujerarsa saboda zargin mulkin kama karya da kusanci da Nyesom Wike
  • Lamarin ya gigita Chinda, inda bai tsaya a ko ina ba sai a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja domin a taka wa takwarorinsa burki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – An fara samun sauki a cikin rikicin da ya dabaibaye ‘yan adawa a majalisar wakilan tarayya bayan da Shugaban majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya shiga tsakani.

Shugaban Marasa Rinjaye, Kingsley Chinda, wanda ke wakiltar mazaɓar Obio Akpor ta Jihar Ribas, ya fuskanci barazana na tsige shi daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi sabon nadi a hukuma sakamakon karin kwamishinoni a Kano

Shugaban Majalisar Wakilai a shiga batun tsige Chinda
Hoton Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas Hoto: Abbas Tajudeen
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa wasu daga cikin 'yan jam'iyyun marasa rinjaye a majalisa sun yi zargin cewa yana gaban kansa wajen gudanar da ayyukan da ya kamata a gana a kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An so tsige Hon. Chinda a majalisa

Rahotanni sun ce wasu daga cikin ‘yan majalisa sun zargi Chinda da kusanci da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wanda ake ganin abokin Shugaba Bola Tinubu ne.

Lokacin da ya samu labarin cewa ana shirin tsige shi, Chinda ya garzaya kotun tarayya da ke Abuja makon jiya domin taka wa takwarorinsa burki a nan take.

Ya shaida wa kotun cewa duk wani yunkuri da ya taimaka aka tsige shi, abu ne da ya saba da doka da tsarin mulki da ya ba shi damar mu'amala da wanda ya so.

Shugaban majalisa ya shiga tsakani

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da wata ganawa a Abuja ranar Litinin da daddare, wacce Shugaban Majalisar, Tajudeen Abbas ya halarta don sasanta rikicin.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke a Majalisar Wakilai a yunƙurin tsige shugaban marasa rinjaye

Wani daga cikin ‘yan majalisar da ya halarci taron ya bayyana cewa shiga tsakani da Rt. Hon. Abbas ya yi, ya taimaka wajen cimma sulhu na ɗan lokaci.

An dakata da batun tsige Chinda
Hoton wasu daga cikin 'yan majalisar wakilai Hoto: House of Rrepresentatives
Source: Facebook

Ya ce:

“Mun yi zama na kusan awa uku, muna ta muhawara sosai. Wasu daga cikinmu sun so a tsige duka shugabannin ‘yan adawa gaba ɗaya, musamman daga yankin Arewa da Yammacin Najeriya. Amma Kakakin ya roƙi a ba shi lokaci domin ya sasanta lamarin.”
“Da ba a shiga tsakani ba, da lamarin ya yi muni sosai."

A cewar wani majalisa, Chinda ya nemi afuwa ga yadda ya kai ƙara kotu, ya kuma yi alkawarin janyewa domin ba da dama a sasanta cikin ruwan sanyi.

A halin yanzu, ana sa ran 'dan majalisar zai ci gaba da ganawa da wasu daga cikin ‘yan adawa domin ƙara samun goyon baya da tabbatar da matsayinsa na jagoransu.

Majalisa ta yi magana a kan zaben 2027

A baya, mun wallafa cewa Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da niyyar ganin cewa zabukan 2027 sun inganta.

Kara karanta wannan

Kudirin sauya tsarin zaben Najeriya na kara ƙarfi a majalisa, an fadi amfanin da zai kawo

Ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar ziyarar wata tawagar Tarayyar Turai a Abuja, inda ya ce gwamnati na aiki tukuru wajen tabbatar da zabe mai adalci.

Ya kara da cewa majalisar dokoki — wadda ta ƙunshi majalisar dattawa da wakilai — na gudanar da taruka don tsara gyare-gyare ga Dokar Zabe ta 2022

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng