Dattawan Arewa Sun Bayyana Matsayarsu kan Zaben 2027, Ta Fadi Kalan Dan Takararta

Dattawan Arewa Sun Bayyana Matsayarsu kan Zaben 2027, Ta Fadi Kalan Dan Takararta

  • Kungiyar Dattawan Arewa, ACF ta yi magana kan layin da za ta kama game da zaben shekarar 2027 da ke tafe a Najeriya.
  • Dattawan suka ce za su zama kungiya wacce ba za ta nuna bangaren siyasa ba, kuma ba za ta goyi bayan jam’iyya daya ko dan takara ba
  • ACF ta yaba wa jami’an tsaro bisa sadaukarwarsu da kuma ta bukaci gwamnati ta dakile matsalar da ke addabar kamfanin Dangote

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Yayin da zaben 2027 ke kara gabatowa, Kungiyar dattawan Arewa, Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi magana game da zaben.

Kungiyar ACF ta sake nanata cewa tana zaman kungiyar dattawa ce mai zaman kanta ba tare da nuna wani bangare na siyasa ba.

Dattawan Arewa sun magantu kan zaben 2027
Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar ACF, Alhaji Bashir Dalhatu. Hoto: Waziri Studio.
Source: Facebook

Batutuwan da ACF ta tattauna kansu a Kaduna

Kara karanta wannan

'Da Allah na dogara': Abba kan barazanar da ake yi masa game da zaben 2027

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu (Wazirin Dutse), ya bayyana haka ne a taron da aka gudanar a hedikwatar ACF a Kaduna, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata 7 ga watan Oktoban 2025, an tattauna kan abubuwa biyu; dokar sadarwa tsakanin jami’an kungiyar da kuma shirye-shiryen bikin cika shekara 25 da kafa ACF.

Dalhatu ya ce kungiyar ta damu da yadda wasu jiga-jigan ta ke fitar da bayanai masu karo da juna a kafafen yada labarai, abin da ke iya rage karfinta da hadin kanta.

A cewarsa:

“Ko da yake mambobinmu na iya zama cikin jam’iyyun siyasa, ACF ba za ta taba goyon bayan jam’iyya daya ba. Abin da muke yi shi ne bayyana irin halayen da ake bukata ga wanda ke neman mulki.”

Ya kara da cewa babbar manufar kungiyar ACF ita ce kare dimokuradiyya, tabbatar da nagartaccen mulki, da hadin kan Najeriya.

Dalhatu ya kuma yi gargadin cewa yawaitar kirkirar sababbin kungiyoyi masu kama da ACF a Arewa ba abin da zai kawo cigaba ba, yana mai cewa “karfinsu yana cikin hadin kai da magana da murya daya.”

Kara karanta wannan

Akpabio ya yi maganar farko bayan bude majalisa da dawowar Sanata Natasha

Ya tuna cewa lokacin da aka kafa ACF a shekarar 2000, shugabannin Arewa sun hada kai daga bangarori daban-daban domin samar da kungiya daya da za ta kare muradun yankin.

Dattawan Arewa sun nuna damuwa kan rikicin da ke faruwa a matatar Dangote
Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Dangote Industries.
Source: Getty Images

ACF ta magantu kan tsaro, rikicin matatar Dangote

A bangaren tsaro, Dalhatu ya yabawa sojoji da jami’an tsaro bisa sadaukarwarsu wajen yaki da ta’addanci da ‘yan bindiga a Arewa, tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwa.

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki mataki kan rikicin da ke tattare da matatar Dangote, yana cewa wannan lamari “babbar illa ce ga kasa” da ke bukatar a dakile ta cikin gaggawa.

Rahoton The Nation ya ce Dalhatu ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin mambobin kungiyar, yana mai cewa:

“Mu ci gaba da magana da murya daya, mu kare hadin kanmu, mu yi aiki don cigaban yankin Arewa da Najeriya baki daya.”

Dattawan Arewa sun 'gano' masu son karya Dangote

Mun ba ku labarin cewa kungiyar ACF ta bayyana damuwa kan wani yunkuri da ake zargi na hana matatar Dangote aiki yadda ya kamata.

ACF ta ce wannan dambarwar na iya lalata tattalin arzikin Najeriya da kuma hana masu zuba jari shigowa ƙasar.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai za ta kafa dokoki kan POS da Kirifto a Najeriya

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta kare matatar man daga munanan makirce-makirce na cikin gida da na waje.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.