Shirin 2027 Ya Kankama, Jagororin Jam'iyyar Hadaka, ADC Sun Sa Labule a Abuja
- Shugabannin jam'iyyar ADC sun gana a Abuja yau Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025 a wani bangare na shirye-shiryen zaben 2027
- Shugaban ADC na kasa, David Mark da sakataren jam'iyyar, Rauf Aregbesola da manyan jagororin hadakar adawa sun halarci taron
- David Mark ya musanta zargin da ake cewa sun kulla kawance saboda kwadayin mulki, yana mai cewa burinsu ceto Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Manyan jagororin jam'iyyar hadaka watau ADC sun shiga ganawa ta musamman a babban birnin tarayya Abuja yau Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa taron na gudana ne a sirrince kuma an ga manyan kusoshin ADC sun shiga dakin taron ciki har da mukaddashin shugaban jam'iyya, Sanata David Mark.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren ADC na kasa, Rauf Aregbesola, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, da tsohon gwamnan Jihar Edo, Osaheimen Osunbor sun halarci taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ADC ya soki salon 'yan siyasa
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban jam’iyyar ADC kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya zargi ‘yan siyasa da kafa gwamnati domin su ci moriya kadai.
Ya yi alkawarin cewa wannan hadaka, “za ta sauya wannan tsohon tsarin. Dole mu kawo sabon yanayin shugabanci a kowane fannoni, gwamnati, kasuwanci da al’umma"
A lokacin da yake magana da mambobin NWC kafin shiga taron, David Mark ya ce manufarsu ba wai kawai su karɓi mulki a 2027 ba ne, burinsu su kawo sauyi ga al'umma.
“Manufarmu ita ce mu bar gado wanda jikokinmu za su yi alfahari da shi. Wannan tsere ne mai tsayi wanda dole mu fafata kuma mu yi nasara. Babu batun faduwa a ranmu," in ji shi.
Abubuwan da jam'iyyar ADC ta sa a gaba
Shugaban jam’iyyar ADC ya kuma bayyana cewa akwai muhimman ayyuka a gaban kwamitin gudanarwa na ƙasa
A rahoton a Vanguard, Sanata Mark ya ce:
"Wajibi mu canza kundin tsarin mulkin jam'iyya domin ya dace da sabon yanayi, mu samar da dokoki, ƙa’idojin kuɗi da tsarin bin doka.
"Ya wajaba mu kafa tsarin aiki mai karfi tun daga mazabu, kananan hukumomi da jihohi tare da masu tsare-tsare, rijistar zama dan jam'iyya da ofisoshin jam'iyya."

Source: Facebook
David Mark ya bayyana cewa ADC za ta shirya tunkarar kowane zabe da nufin samun nasara kuma za ta tsayar da nagartattun yan takara, wadanda ba za su ba jama'a kunya ba.
"Za mu tsayar da ‘yan takara nagari, wadanda cancanta suka cika ginshiƙai huɗu, halayya, kwarewa, jarumta, da Ladabi."
Jam'iyyar ADC ta soki Tinubu kan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta soki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a sassan Najeriya.
ADC ta caccaki Tinubu bisa abin da ta kira rashin nuna damuwa da halin rashin tsaro da kasar nan ke ciki, tana mai cewa ya fi maida hankali kan tarurrukan siyasa.

Kara karanta wannan
"Ka saurari matarka": Kusa a APC ya ba Jonathan shawara kan takara da Tinubu a 2027
Ta bayyana cewa abubuwan da shugaban kasan ya yi tun bayan hawansa mulki, sun nuna cewa bai san hanyar warware matsalolin Najeriya ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

