'Tinubu Ya Fi Ƙarfinka,' Ɗan takarar gwamna ya gargadi Jonathan kan takarar 2027

'Tinubu Ya Fi Ƙarfinka,' Ɗan takarar gwamna ya gargadi Jonathan kan takarar 2027

  • Dr. Abdul-Azeez Adediran (Jandor) ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da kada ya tsaya takara a zaben 2027
  • 'Dan takarar gwamnan a 2023 ya ce mutane na rudar Jonathan kan yin takara da Bola Tinubu, yana mai cewa zai fadi ba nauyi
  • Jandor ya bayyana dalilan da suka sanya Tinubu ya zama gogaggen ɗan siyasa da ba za a iya kayar da shi a zaben 2027 ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Dr. Abdul-Azeez Adediran (Jandor), ya gargadi tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da kada ya saurari masu cewa ya fito takara a zaben 2027.

Jandor, shi ne Jagoran Lagos4Lagos Movement, kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Lagos karkashin jam’iyyar PDP a 2023.

An shawarci Jonathan ya hakura da takara a 2027
Shugaba Bola Tinubu na gaisawa da Goodluck Jonathan a wani taro. Hoto: @GEJonathan
Source: Twitter

"Suna rudarsa" - Jandor kan takarar Jonathan

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya kama kansa a kan zarginsa da takardun karatun bogi

Yayin wata tattaunawa da NAN a Legas a ranar Lahadi, Jandor ya ce idan Jonathan ya amince da wannan kira, zai sha babbar kunyar siyasa domin “Tinubu zai kayar da shi cikin sauƙi.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jandor ya ce:

“Mutanen da ke kira gare shi da ya tsaya takara suna ruɗarsa ne. Tinubu ba mutum ba ne da za a iya kayar da shi a zaben 2027. Gogaggen ɗan siyasa ne, kuma ya fi Jonathan kwarewa."

Ya kara da cewa:

“Tinubu ya taba kayar da Jonathan daga wajen Aso Villa, yanzu kuma yana zaune a ciki. Don haka ba dai dai ba ne a zo ana kokarin hada karfinsu yanzu."

Tsohon dan takarar gwamnan, Jandor ya ce akwai bambanci tsakanin mutumin da “ya samu shugabanci ta hanyar aiki tukuru” da wanda “ya hau mulki bisa tsautsayi ba.”

An kawo bambancin Tinubu da Jonathan

Dr. Abdul-Azeez Adediran (Jandor) ya ce:

“Mutumin da ya farka da safe ya tsinci kansa a matsayin shugaban ƙasa ba zai iya yin gogayya da wanda ya yi aiki tukuru, ya sha wahala, kuma ya yi nasara kan 'yan adawa ba."

Ya jaddada cewa tsohon shugaban kasar zai fadi babu nauyi idan ya yi yunkurin sauke Tinubu daga mulki, saboda a cewarsa, Tinubu yanzu yana da ƙarfi, shahara da gogewa da suka wuce na Jonathan.

Kara karanta wannan

"Ka saurari matarka": Kusa a APC ya ba Jonathan shawara kan takara da Tinubu a 2027

Jaridar Punch ta rahoto tsohon gwamnan ya ce akwai bukatar Jonathan ya saurari matarsa, Patience Jonathan, wacce ta taba shawartarsa a kan kada ya sake tsayawa takara.

“Idan akwai wanda ya fi sanin abin da ya dace da shi, to matarsa ce. Ya kamata ya saurare ta,” in ji Jandor.
Tsohon dan takarar gwamnan Legas, Jandor ya ce babu wanda zai iya kayar da Tinubu a 2027
Hoton tsohon dan takarar gwamnan Legas, Jandor da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @officialjandor, @officialABAT
Source: Facebook

An yaba da tsare-tsaren tattalin arzikin Tinubu

Jandor ya yabawa Shugaba Bola Tinubu saboda sauye-sauyen tattalin arzikin da ya kawo, yana mai cewa “sun fara haifar da sakamako mai amfani.”

“Ba mu ce komai ya gyaru ba, amma shugaban ƙasa ya nuna jarumta wajen kwace albarkatun ƙasa daga hannun wasu ‘yan kalilan da suke cin gajiyar tallafin mai, ya mayar da shi ga ƙasa, jihohi da kananan hukumomi."

- Dr. Abdul-Azeez Adediran (Jandor).

Ya ce sabon tsarin rabon kuɗin FAAC ya ninka sau uku, abin da ke ba jihohi da kananan hukumomi damar aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma.

Yadda aka ci amanar Goodluck a 2015

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ya fadi zaben 2015 ne saboda cin amanar wasu 'yan siyasar kasar nan.

Kara karanta wannan

Tazarce: An zakulo manyan abubuwa 6 da za su taimaka wa Tinubu ya ci zabe a 2027

Jonathan ya bayyana haka ne a bikin cika shekaru 70 da haihuwa na tsohon shugaban ma’aikatan fadarsa, Mike Oghiadomhe.

Tsohon shugaban kasar ya yi bayanin halayen 'yan siyasar Najeriya, musamman na rashin gaskiya da kuma saurin cin amanar mutum.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com