Rikici Ya Ɓarke a Majalisar Wakilai a Yunƙurin Tsige Shugaban Marasa Rinjaye

Rikici Ya Ɓarke a Majalisar Wakilai a Yunƙurin Tsige Shugaban Marasa Rinjaye

  • Shugaban Matasan Rinjaye a Majalisar Wakilai, Kingsley Chinda, ya shiga matsala bayan takwarorinsa sun taso shi a gaba
  • Yanzu haka, dambarwa ta kaure a yayin da ake yunƙurin yadda za a tsige shi daga mukaminsa saboda wasu dalilai
  • ‘Yan majalisa daga jam’iyyun adawa sun shirya zama na gaggawa domin tattauna rikicin cikin gida da ya mamaye su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wani sabon rikici ya bullo a Majalisar Wakilan yayin da wasu daga cikin‘yan majalisa daga jam’iyyun adawa ke zargin ana shirya wa Shugaban marasa rinjaye makarkashiya.

Ana zargin shirye-shiryen cire Shugaban jam'iyyun adawa a zauren, Hon. Kingsley Chinda ya yi nisa, lamarin da bai yi wa masa dadi ba.

Sabon rikici ya kunno cikin majalisar wakilai
Hoton 'yan majalisar wakilai a zaman majalisa Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wannan na zuwa ne yayin da Majalisar ke shirin dawowa daga hutu na tsawon watanni biyu da ta tafi.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji dalilin da ya sa Atiku Abubakar ke jan kafa kan batun takara a 2027

Ana shirin koma wa zaman majalisa

Majalisar za ta ci gaba da zama gobe, Talata 7 ga Oktoba, 2025 bayan dage ranar hutu da shugabanninta suka a yi a watan Satumba, 2025.

'Yan adawa a majalisar sun hada da wakilan PDP, LP, NNPP, ADC, SDP, APGA da YPP, kuma ana hasashen rikici ya ratsa a tsakaninsu gabanin dawo wa daga hutu.

Ana fargabar tsige Kingsley Chinda
Hoton wasu daga cikin 'yan majalisar wakilai Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

Wata majiya ta bayyana wa jaridar cewa babban ƙorafi a kan Chinda shi ne rashin kiran taro tsakanin ‘yan majalisar jam'iyyun adawa na tsawon sama da shekaru biyu.

Wasu sun ce hakan ya jawo rashin fahimtar juna da rashin haɗin kai a ƙungiyar tsakanin jam'iyyun da ba sa da mulki a sama.

Wani ɗan majalisa ya ce:

“Tun da aka kafa wannan majalisa, babu wani taro da aka kira. Shi kaɗai yake yanke hukunci, ba mu san abin da ke faruwa ba.”

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna ya fusata, ya ajiye mukami bayan sauya shekar Eno zuwa APC a Akwa Ibom

Shugaba a majalisa, Chinda ya garzaya kotu

Chinda, wanda ke wakiltar mazabar Obio/Akpor a Jihar Ribas karkashin PDP, ya kai ƙara gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin neman hana cire shi daga kujerar.

Ya zargi wasu wakilai da shirin cire shi saboda kusancinsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike da ke goyon bayan Bola Tinubu duk da yana PDP.

A ƙarar da lauyansa J.Y. Musa (SAN) ya shigar, Chinda ya nemi kotu ta hana Majalisar Wakilai, Kakakin Majalisa, da jam’iyyun da yin wani abu da zai sa a cire shi. Ya ce wannan shirin cire shi da ake yi mataki ne sa ya sabawa tsarin Majalisa da kundin tsarin mulkin Najeriya

Majalisa: Chinda ya fusata takwarorinsa

Shugaban ƙungiyar PDP a Majalisa, Fred Agbedi, ya tabbatar da cewa akwai rashin tattaunawa tsakanin ‘yan adawa, amma ya musanta maganar cewa ana shirya cire Chinda.

Ya ce Kakakin Majalisa, Abbas Tajudeen, ya riga ya shiga tsakani domin sasanta rikicin da ya ratsa a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun kona gidan basarake a Binuwai, sun bayyana dalilinsu

Yayin da rikicin ke ƙaruwa, an shirya taron gaggawa na dukkanin ‘yan ƙananan jam’iyyu a yau Litinin 06 ga watan Oktoba, 2025 a Abuja.

Wasu shugabannin jam’iyyun adawa, ciki har da Agbedi (PDP), Afam Ogene (LP), Muktar Umar-Zakari (NNPP), da Peter Uzokwe (YPP), sun rattaba hannu a sanarwar taron.

A cewar sanarwar, zai tattauna:

“Ci gaban da ake samu a cikin shugabancin ƙananan jam’iyyu, musamman ƙarar da Chinda ya shigar da nufin dakatar da sauran ‘yan adawa daga cire shi daga muƙaminsa.”

Majalisa ta magantu a kan zaben 2027

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na son a yi sahihin zaɓe a 2027.

Rt. Hon Abbas ya kafa hujja da cewa gwamnatin tarayya ta jajirce wajen inganta tsarin dimokuraɗiyya ta hanyar tabbatar da gaskiya, adalci da inganci a tsarin zaben ƙasa.

Shugaban majalisar ya ce an riga an fara matakan sauye-sauye a dokar zabe ta 2022 domin tabbatar da cewa sabon tsarin zabe zai yi daidai da ƙa’idodin ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng