Wata Sabuwa: Jigon APC Ya Bukaci Dangote Ya Buga Takara da Tinubu a 2027

Wata Sabuwa: Jigon APC Ya Bukaci Dangote Ya Buga Takara da Tinubu a 2027

  • Malam Salihu Isa Nataro ya bukaci ‘yan Najeriya su duba yiwuwar takarar Aliko Dangote da Gwamna Alex Otti a 2027
  • Ya ce Dangote da Otti na da kwarewa wajen gudanar da harkokin tattalin arziki da mulki da za su iya dawo da martabar ƙasar
  • Nataro ya yaba da tsarin mulkin gwamna Otti a jihar Abia tare da kira ga Dangote da ya shiga siyasa domin ci gaban Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wani jigon jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Kebbi, Malam Salihu Isa Nataro ya fara kiran Aliko Dangote ya shiga siyasa.

Nataro ya bayyana cewa tikitin shugabancin ƙasa tsakanin Alhaji Aliko Dangote da Gwamna Alex Otti na Abia zai iya zama mafita ga matsalolin tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Domin samun sauki,' Ana neman Tinubu ya saka wa talaka tallafi a abubuwa 3

Alex Otti da Aliko Dangote
Gwamnan Abia, Alex Otti da Aliko Dangote. Hoto: Dangote Industries|Abia State Government
Source: Facebook

Tribune ta wallafa cewa ya ce hadin gwiwar masana tattali irin Dangote da gogaggen mai mulki kamar Otti zai taimaka wajen rage talauci, samar da ayyukan yi da farfaɗo da masana’antu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nataro ya yi wannan bayani ne a wata ganawa da ‘yan jarida a Abuja, inda ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugabanni masu hangen nesa da gaskiya wajen tafiyar da tattali.

Ana neman Aliko Dangote ya yi takara

Malam Nataro ya bayyana cewa idan har Dangote zai ajiye sauran mukamansa a kamfanoninsa domin hidimar ƙasa, ‘yan Najeriya za su goyi bayan takararsa tare da Gwamna Otti.

Ya ce dukkansu sun nuna bajinta a fannin gudanar da harkokin kasuwanci da shugabanci, abin da zai iya dawo da martabar Najeriya.

Vanguard ta wallafa cewa ya ce:

“Dangote na da gogewa wajen sarrafa masana’antu, yayin da Otti ya tabbatar da cewa ana iya tafiyar da mulki cikin gaskiya da hangen nesa,”

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun fadi mutanen da ke son durkusar da matatar Dangote

Jigon APC ya yabi gwamna Alex Otti

Jigon na APC ya yabawa gwamna Otti saboda yadda yake tafiyar da al’amuran mulki da tsari mai nagarta a jihar Abia.

Nataro ya kuma bayyana cewa idan Otti ya samu shugabancin ƙasa, zai ƙarfafa hukumomin yaƙi da rashawa kamar EFCC da ICPC don tabbatar da gaskiya a gwamnati.

Dangote da Tinubu a matatar shi da ke Legas
Dangote da Tinubu a matatar shi da ke Legas. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Nataro ya ce Tinubu ya yi kokari

Nataro ya yaba da ƙoƙarin shugaba Bola Tinubu wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, amma ya nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati ba su nuna himma.

Ya jaddada cewa Najeriya tana bukatar shugabanni masu gaskiya da ƙwarewa, ba masu siyasar babakere ba.

A cewarsa:

“Kasar nan tana bukatar shugabanni masu tausayi da hangen nesa — wanda tikitin Dangote–Otti zai iya wakilta.”

Malam Nataro ya kuma yi kira ga gwamnati ta rage kashe kuɗi da kuma tsaurara hanyoyin karɓar haraji.

Irin zaben da Tinubu ke so a 2027

Kara karanta wannan

Gwamna ya lallaba ya gana da Tinubu, za a saki jagoran 'yan ta'adda da Buhari ya kama a 2021

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya yi magana kan zaben shekarar 2027.

Abbas ya bayyana cewa a shirye gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta ke wajen gudanar da sahihin zabe a kasar.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne yayi ganawa da tawagar tarayyar Turai da ta ziyarci Najeriya kan gyaran zabe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng