‘Za a Maimata June 12’: Malami a Kaduna Ya Yi Hasashe Mai Ban Tsoro kan Zaben 2027
- Wani malamin addini daga Kaduna ya bayyana wani mafarki da ya yi mai ban tsoro musamman game da zaben shugaban kasa a Najeriya
- Matashin Faston, Godwin Auta Musa, ya ce ya samu wahayi cewa zaben 2027 zai yi kama da zaben June 12 na shekarar 1993
- Ya ce cikin mafarki ya ga dan takara ya yi nasara amma gwamnati ta soke sakamakon, yana kira ga ‘yan kasa su tashi tsaye da addu’a
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Matashin malamin addinin Kirista ya yi hasashen abin bakin ciki da zai faru a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 a Najeriya.
Fasto Godwin Auta Musa wanda limamin coci ne ya bayyana wani wahayi da ya samu wanda ya shafi zaben Najeriya na shekarar 2027.

Source: Facebook
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na Facebook, Fasto Musa ya ce ya yi mafarki inda aka nuna masa abin da zai faru a lokacin zaben gaba.

Kara karanta wannan
Lambar Abba Kabir ta fito, malamin addini ya jero gwamnoni 4 da ka iya komawa APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Fastoci ke hasashen zaben 2027
Yayin da ake ta shirye-shiryen zaben shekarar 2027 da ke tafe, malaman addinin Kirista suna yawan fadin abin da zai faru game da zaben.
Wasu daga cikinsu har hasashen wanda zai lashe zaben suke yi da suke cewa sun gani a mafarki ko kuma kamar wahayi da aka saukar musu.
Har ila yau, ana yawan gargadin wasu yan siyasa da ka da ma su sha wahalar fitowa takara a zaben saboda an hango musu rashin nasara.
Fasto ya yi hasashe kan zaben 2027
Matashin Faston ya ce zaben zai kasance mai kama da na June 12, 1993 wanda aka soke a baya inda ya tabbatar da haka da cewa ya kamata a dage da addu'o'i.
Ya bayyana cewa cikin mafarkin nasa, dan takara ya lashe zaben, amma gwamnatin da ke mulki ta soke sakamakon.

Source: Facebook
'Yadda zaben shugaban kasa a 2027 zai wakana'

Kara karanta wannan
Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi
Har ila yau, ya ce lamarin zai yi kama da abin da ya faru tsakanin MKO Abiola da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida a shekarar 1993.
Faston ya ce:
“Na yi mafarki cewa zaben 2027 zai zama kamar na June 12, 1993, dan takara ya ci zabe amma shugaba mai ci zai soke sakamakon.
"Don haka, mu tashi mu yi addu’a domin nufin Ubangiji ya tabbata.”
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya su roƙi Allah don samun zaman lafiya da adalci a lokacin zabe, domin a tabbatar da abin da Allah ya tsara ga ƙasar.
An yi hasashen Abba zai koma APC
Kun ji cewa babban malamin addinin Kirista, Elijah Ayodele ya yi hasashe mai ban mamaki game da wasu gwamnonin adawa da za su iya komawa APC mai mulkin Najeriya.
Malamin ya gargadi ga shugaban kasa, Bola Tinubu cewa wasu gwamnonin adawa za su koma APC amma ba duka ne ke son taimaka masa inda ya ce dole ne ya yi taka-tsantsan.
Limamin daga cikin gwamnonin akwai na Kano, Zamfara, Enugu da Taraba wanda wasu a cikinsu za su shiga jam’iyyar ne kawai don su sami albarkar shugaban ƙasa da kuma neman mukamai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng