Matasa Sun Yi Gangami kan Tituna, Sun Fadi Matsayarsu kan Tazarcen Tinubu a 2027

Matasa Sun Yi Gangami kan Tituna, Sun Fadi Matsayarsu kan Tazarcen Tinubu a 2027

  • Matasan jam’iyyar APC a jihar Oyo sun bayyana goyon bayansu ga takarar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027 mai zuwa
  • Matasan sun bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin “Tattakin Goyon Baya” da kungiyar matasan ta shirya a birnin Ibadan
  • Kungiyar matasan ta yi alkawarin cewa za ta jagoranci nasarar jam’iyyar a zaben 2027 domin dorewar shirin Renewed Hope

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Matasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Oyo sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Matasan sun amince shugaban kasar ya fito takara a zaben 2027, yayin da suka jaddada biyayyarsu ga shirin Renewed Hope na gwamnatin Tinubu.

Matasa sun fito gangamin nuna goyon baya ga tazarcen shugaban kasa Bola Tinubu a jihar Oyo.
Hoton matasan APC yayin da suka fito gangamin nuna goyon baya ga Tinubu a Oyo. Hoto: Fagbemi Abodunrin Aminah
Source: Facebook

Oyo: Matasa sun yi gangami don Tinubu

Jaridar The Punch ta rahoto cewa matasan sun bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin “Tattakin Goyon Baya” da kungiyar matasan ta shirya a birnin Ibadan.

Kara karanta wannan

'Ba jana'izar mahaifiyar shugaban APC ta kai Tinubu Jos ba,' Atiku ya yi fallasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa dubban matasan jam'iyyar APC daga kananan hukumomi 33 suka halarci wannan tattaki domin nuna hadin kai da shugabancin jam’iyyar.

Gangamin, wanda Ayobami Dagilogba, mai kula da kungiyar matasan APC a jihar, ya jagoranta, ya mayar da manyan titunan Ibadan cikin launin jam’iyyar yayin da matasa suka yi tattaki domin nuna amincewa da gwamnatin Tinubu da shugabancin APC.

“APC ce ke da nasara a 2027” – Matasa

Dagilogba ya bayyana tattakin a matsayin “sako mai ƙarfi da ke cike da aminci da jajircewa” ga duk wasu tsare-tsaren Tinubu.

“Wannan tattaki ba gangami ba ne kawai ba; alamar yakini ce ga shirin Renewed Hope da kuma nufinmu na tabbatar da ci gaban wannan shiri a jihar Oyo da ma kasa baki ɗaya.
“Da taimakon Ubangiji, muna da yakinin cewa jam'iyyar APC za ta samu cikakkiyar nasara a zabukan 2027 da ke tafe.”

- Ayobami Dagilogba.

Kara karanta wannan

Tazarce: An zakulo manyan abubuwa 6 da za su taimaka wa Tinubu ya ci zabe a 2027

Ya ce kungiyar za ta ci gaba da wayar da kai da gina goyon bayan matasa a kowane yanki na jihar, yana mai jaddada cewa matasa su ne “jigon siyasa a kasar”.

Matasan APC a Oyo sun nuna cewa za su tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a 2027
Hoton Shugaba Bola Tinubu a dakin taron TICAD 9 da aka gudanar a Japan. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Gangamin matasa gabanin zaben 2027

Matasan da suka fito gangamin, sun bayyana tattakin a matsayin wata babbar alama ta haɗin kai da sabunta goyon bayansu ga jam’iyyar APC a jihar Oyo.

Sun ce wannan gangami ya nuna kudirin su na ci gaba da tsaya wa tare da shugaban ƙasa Tinubu da jagorancin jam’iyyar wajen kawo ci gaba mai ɗorewa a jihar da kasa baki daya.

A zaben 2023, Tinubu ya doke tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar LP.

Ana sa ran Atiku Abubakar da Peter Obi za su iya sake tsayawa takara a zaben shugaban ƙasa na 2027 mai zuwa, don kalubalantar Tinubu da APC.

Irin zaben da Tinubu yake so a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce Bola Tinubu na da niyyar tabbatar da gaskiya da inganci a zabukan 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sahihancin zaben 2027 da tawagar tarayyar Turai

Majalisar dokoki ta tarayya dai na aiki kan sauya dokar zabe ta 2022 domin magance matsalolin da aka fuskanta a zaben shekarar 2023.

Rahotanni sun nuna cewa Hon. Tajudeen Abbas ya yi wannan maganar ne yayin ganawa da shugabannnin EU a Abuja, inda ya yabi shirye-shiryen Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com