Tsofaffin Kansilolin Kano Sun Gana da Barau bayan Abba Ya ba Su Biliyoyin Naira
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya biya tsoffin kansiloli 1,198 na jihar Kano hakkokinsu da suka kai Naira biliyan 5.6
- Sanata Barau Jibrin ya karɓi tawagar tsofaffin kansiloli daga Rimin Gado a ofishinsa da ke majalisar dattawa, Abuja
- Tsoffin kansilolin da yawansu ’yan APC ne sun gode wa gwamnan saboda adalcin da ya nuna duk da bambancin siyasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi tawagar wasu tsofaffin kansiloli daga ƙaramar hukumar Rimin Gado ta jihar Kano a Abuja.
Ziyarar ta zo ne jim kaɗan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya biya wasu tsofaffin kansilolin jihar Naira biliyan 5.6 na hakkokin da suka jima suna bi.

Source: Facebook
Barau ya wallafa a Facebook cewa ya tattauna da tawagar kan ci gaban al’umma da jihar Kano baki ɗaya tare da tabbatar da goyon bayansa ga jama’ar yankinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ziyarar tsofafin kansiloli ga Barau Jibrin
Tawagar tsofaffin kansilolin ƙarƙashin jagorancin sakatarensu, Hon. Ibrahim Jemomi, ta ziyarci Sanata Barau da wasu ’yan majalisar dattawa biyu, Muntari Dandutse da Babangida Hussaini.
Sanata Barau Barau ya ce sun tattauna kan hanyoyin inganta ci gaban mazabu, jihar Kano, da ƙasa baki ɗaya.
A cewarsa:
“Mutanenmu su ne ƙarfinmu, kuma za mu ci gaba da zama tare da su a kowane lokaci.”
Gwamna Abba ya biya tsofaffin kansiloli
A gefe guda, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya biya tsofaffin kansiloli 1,198 hakkokinsu da suka kai Naira biliyan 5.6.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa wannan shi ne zagaye na biyu na biyan basussukan da aka gada daga gwamnatin da ta gabata.
A watan Mayun 2025, gwamnan ya riga ya biya tsofaffin kansiloli 903 na farko da Naira biliyan 1.8, inda ya sha alwashin kammala sauran bashin da ya rage kafin ƙarshen shekarar 2025.

Kara karanta wannan
Matasa sun yi zanga zangar tir da kalaman Gwamnan Kano na a cire kwamishinan 'yan sanda
Dalilin biyan kansiloli hakkokinsu
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na alkawuransa na adalci da gaskiya ga tsofaffin ma’aikata da suka yi hidima ga al’umma.
Sanusi Bature ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya ce an biya kudin ne domin yin adalci ga waɗanda suka sadaukar da kai don cigaban ƙananan hukumomi.
Gwamnan ya kuma ja hankalin masu cin gajiyar da su yi amfani da kuɗin don tallafawa iyalansu da al’ummominsu.

Source: Facebook
A lokacin biyan kuɗin, tsofaffin kansilolin da yawansu ’yan jam’iyyar APC ne sun bayyana godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda nuna adalci duk da bambancin siyasa.
Abba ya raba wa matasa kudi a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya raba makudan kudi ga wasu matasan jihar.
Rahotanni sun nuna cewa sama da Naira miliyan 800 gwamnan ya raba domin inginta rayuwar matasan Kano.
Binciken Legit Hausa ya gano cewa sama da matasa 5,000 ne suka shiga tallafin da gwamnatin jihar Kano ta raba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

