2027: Manyan ‘Dalilai’ 5 da Ka Iya Sanya Kwankwaso Komawa APC Gaba Daya
- Rahotanni sun yi ta yawo cewa Rabiu Musa Kwankwaso zai iya barin NNPP zuwa APC kafin zaben 2027, abin da zai girgiza siyasar Najeriya gaba daya
- Masana sun ce Kwankwaso na da karfin kuri’u sama da miliyan biyar a Kano, kuma shiga APC zai taimaka wa Shugaba Tinubu wajen sake lashe zabe
- Tsohon gwamnan ya jaddada cewa sauya shekar sa za ta kasance da sharudda, ciki har da mukamai da albarkatun gwamnati ga Kwankwasiyya da magoya bayansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya kasance jagora kuma jigon tafiyar Kwankwasiyya wanda ke da tasiri a Arewacin Najeriya.
An yi ta yada jita-jita a kwanan nan cewa Sanata Kwankwaso na iya barin NNPP ya koma APC kafin 2027.

Source: Twitter
Rahoton Punch ya nuna cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, yana iya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC kafin babban zaben 2027.
Legit Hausa ta gano cewa Kwankwaso na da goyon bayan talakawa mai karfi a Kano da Arewa, wanda zai iya taimaka wa APC da Tinubu.
Dalilai da ka iya sa Kwankwaso komawa APC
Wannan rahoto ya yi duba kan wasu dalilai guda biyar da masana ke ganin zasu iya sa Kwankwaso yanke shawarar komawa APC kafin 2027.
1. Karfin kuri’unsa a Arewa
Ɗaya daga cikin wadanda ke da goyon bayan talakawa mafi ƙarfi a Arewacin Najeriya shi ne na Rabiu Musa Kwankwaso.
A Kano, ya lashe kananan hukumomi 38 daga cikin 44 a jihar Kano, abin da ya nuna karɓuwarsa a zaben 2023.
Masana sun bayyana wannan nasara tasa a matsayin mai matuƙar tasiri, inda suka ce masu kada kuri’a sama da miliyan biyar na Kano, wanda dan siyasa ne da bai kamata a bar shi hannun adawa ba.
Wasu manyan jiga-jigan APC suna ganin cewa samun goyon bayan Kwankwaso zai iya tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaben 2027.
Saboda tasirinsa mai girma, ana ganin Kwankwaso na iya tattaunawa da jam’iyyar domin a amince da tafiyar Kwankwasiyya da kuma bai wa magoya bayansa damar samun tikiti na takara a karkashin APC.

Source: UGC
2. Alakar Kwankwaso da Tinubu
Komawa jam’iyyar APC za ta ƙarfafa dangantakar Rabiu Kwankwaso da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A watan Yuli 2025, Kwankwaso ya yi wata ganawa ta sirri da Shugaban kasa a Aso Rock, inda ya amince cewa “yana iya yin aiki tare da Tinubu.”
Wasu daga cikin manyan jagororin jam’iyyar sun ma fara tunanin yiwuwar zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa ga Tinubu a zaben 2027.
A kalla ma, shiga cikin APC zai ba shi damar zuwa fadar shugaban kasa kai tsaye, abin da zai ba shi ikon neman mukamai masu muhimmanci, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
3. Neman mukamai da tasiri
Rabiu Kwankwaso ya bayyana a fili cewa duk wata sauya sheka da zai yi dole ne ta kasance da sharuɗɗa.
Ya jaddada cewa ba zai ƙara bari a “yi amfani da shi a watsar” kamar yadda aka yi a shekarar 2015 ba, yana mai cewa akwai bukatar samun tabbaci ga kansa da magoya bayansa.

Kara karanta wannan
2027: Kusa a APC ya yi watsi da Kwankwaso, ya hango yadda APC za ta lashe zabe a Kano
Da wannan tsari, Kwankwaso na tabbatar da cewa shi da tafiyarsa ta Kwankwasiyya za su samu mukaman ministoci, nadin mukamai na tarayya da sauran alfanun siyasa a karkashin jam’iyyar APC.
Ya ce:
“Mun shirya shiga APC amma ƙarƙashin ƙa’idoji da alkawura masu ƙarfi. Ba za mu bari a yi amfani da mu a jefar ba kamar da.”

Source: Twitter
4. Karfi da iko a gwamnatin tarayya
Shiga jam’iyyar APC zai ba Kwankwaso damar samun kasafin kuɗi na tarayya da mukamai, waɗanda za a ɗauka a matsayin ayyuka don al’ummar Kano da ma sauran yankuna.
Shugabannin jam’iyyar sun riga sun buɗe kofa wajen tarbar sa, suna cewa dawowarsa za ta kawo “zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaban tattalin arziki” a jihar.
Tare da goyon bayan APC, Kwankwaso zai samu damar jawo masu zuba jari, kafa makarantu, da gina ababen more rayuwa a Kano, tare da ƙarfafa tushen goyon bayan siyasarsa.
5. Ci gaba da kare tasirin siyasarsa a kasa
Bugu da kari, shiga jam’iyyar APC zai mayar da Kwankwaso ɗaya daga cikin manyan ‘yan siyasa a matakin ƙasa baki ɗaya.
Masu sukar sa suna cewa ci gaba da kasancewa a NNPP yana dakile shi daga sauran manyan ‘yan siyasa, amma shiga jam’iyyar mai mulki zai sanya shi cikin jerin manyan masu tasiri a siyasar Najeriya.
Kwankwaso kansa ya taɓa bayyana cewa har yanzu yana da “abin da zai iya bayarwa a matakin jagoranci na ƙasa.”
Yayin da zaben 2027 ke kara kusantowa, shiga cikin APC zai ba shi damar ko sake neman takara, ko kuma zama mai tasiri wajen zaɓar sabon shugaban ƙasa.
6. Zai iya kawo zaman lafiya a Kano
Har ila yau, akwai wasu dalilai da ake ganin zai iya sanya Kwankwaso komawa APC duba da halin da jihar ke ciki.
Shigan Kwankwaso APC zai iya kawo karshen rigimar sarauta da rashin jituwa tsakanin gwamna da jami'an tsaro.
Bugu da kari, hakan zai kawo zaman lafiya a Kano da kuma gudanar da zabe cikin aminci wanda ka iya ba Abba Kabir Yusuf zabe cikin sauki.
Kano: 'Dan APC ya sha alwashi kan zabe
Mun ba ku labarin cewa wani kusa a jam'iyyar APC a jihar Kano, ya hango yadda za su samu nasara a babban zaben shekarar 2027.
Hon. Seyi Olorunsola ya bayyana cewa APC za ta yi nasara ba tare da goyon bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

Kara karanta wannan
'Yar Najeriya da ta shirya kafa tarihin kwanciya da maza 100 a awa 24 ta canza shawara
'Dan siyasaar ya nuna cewa ya kamata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban APC na kasa, su daina daukar Kwankwaso da wani muhimmanci.
Asali: Legit.ng


