Jonathan Ya Debo Ruwan Dafa Kansa da Ya Jingina Marigayi Buhari da Boko Haram

Jonathan Ya Debo Ruwan Dafa Kansa da Ya Jingina Marigayi Buhari da Boko Haram

  • Kalaman tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan kan marigayi Muhammadu Buhari sun fara tauyar da kura
  • Jonathan ya ce akwai lokacin da Boko Haram ta gabatar da Buhari a matsayin wakilinta a tattaunawar sulhu da gwamnatin tarayya
  • Tsohon kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya ce ikirarin Jonathan ba gaskiya ba ne, wani salo ne na neman kuri'u a 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Malam Garba Shehu, tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya karyata ikirarin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Garba Shehu ya ce ikirarin Jonathan cewa Boko Haram ta taɓa zaɓar Buhari a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar sulhu da gwamnatin tarayya ba gaskiya ba ne.

Malam Garba Shehu.
Hoton tsohon kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu. Hoto: @Garshehu
Source: Twitter

Abin da Jonathan ya fada kan Buhari

Daily Trust ta ce Jonathan ya yi wannan magana ne a wajen ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” wanda tsohon babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya rubuta.

Kara karanta wannan

Jonathan: An fitar da dalilai kan karyata alakar Buhari da Boko Haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya bayyana cewa a lokacin gwamnatinsa an kafa kwamitoci daban-daban domin nemo sulhu, inda ya ce a wani lokaci kungiyar ta nuna Buhari a matsayin wakili.

Garba Shehu ya maida martani ga Jonathan

Sai dai Malam Garba Shehu, a cikin wata sanarwa, ya ce wannan magana “ba gaskiya ba ce”, ya zargi Jonathan da amfani da ita a matsayin dabarar neman ƙuri’u a 2027.

“Idan wannan wani mataki ne na kamfen, muna so mu fada wa Mista Jonathan, cewa ya dauko hanya mara bullewa,” in ji Shehu.

Garba Shehu ya jaddada cewa shugabannin Boko Haram, Muhammad Yusuf ko Abubakar Shekau, ba su taɓa bayyana Buhari a matsayin wakilinsu na sulhu ba.

A cewarsa, Shekau ya soki Shugaba Buhari a lokuta da dama kan lamarin har ma ya yi masa barazanar kisa, im ji rahoton Punch.

An dauki batun harin da aka kai wa Buhari

Kara karanta wannan

'Akwai sauran ƴan ta'adda,' Malami ya fadi kuskuren Tinubu a jawabin 1 ga Oktoba

Ya kuma tuna abin da ya faru a 2014, lokacin da Buhari ya tsallake rijiya da baya daga wani harin bam da Boko Haram ta kai masa a Kaduna.

Malam Garba Shehu ya ce wannan ya nuna cewa Buhari da Boko Haram ba a ahiri balle ma wani ya wakilci wani.

Sai dai tsohon kakakin Shugaban Kasar ya fayyace cewa akwai wani lokaci da aka yada cewa Boko Haram ta nada Buhari a matsayin wakili a tattaunawa da gwamnati.

Shehu ya fadi gaskiyar abin da ya faru

Ya ce labarin ya samo asali ne daga wani ɓangaren kungiyar da ake zargin masu adawa da Buhari ne suka dauki nauyinsu, ta bakin Abu Mohammed Ibn Abdulaziz, wanda ya yi ikirarin cewa shi kwamandan Boko Haram ne a Borno.

Amma daga baya shugabannin kungiyar Boko Haram suka nesanta kansu da wannan ikirari.

Buhari da Jonathan
Hoton Marigayi Muhammadu Buhari a Aso Rock da Goodluck Jonathan. Hoto: @MBuhari, Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Garba Shehu ya karkare da cewa kamata ya yi Jonathan ya nemo wani labari daban idan yana son ya samu karɓuwa a 2027 ba ya jinginawa Buhari karya ba.

Jonathan ya tuna rikicin Boko Haram

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa a wasu lokutan mayakan Boko Haram sun fi sojoji makamai.

Kara karanta wannan

Jonathan ya ce Boko Haram ta taba zabar marigayi Buhari a matsayin wakili

Jonathan ya yi ikirarin cewa rikicin kungiyar ta'addanci ta Boko Haram na da rikitarwa da rudani fiye da yadda mutane ke tsammani.

A cewarsa, dole a yi amfani da tsari da ya haɗa da matakan tsaro, mulki nagari, rage talauci, ƙarfafa matasa, da tabbatar da adalci a cikin al’umma idan ana son maganace Boko Haram.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262