Kudirin Sauya Tsarin Zaben Najeriya na Kara Ƙarfi a Majalisa, an Fadi Amfanin da Zai Kawo

Kudirin Sauya Tsarin Zaben Najeriya na Kara Ƙarfi a Majalisa, an Fadi Amfanin da Zai Kawo

  • Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa ana shirin yin gyaran kundin tsarin mulki kan zabe
  • Hon. Abbas ya ce shirin gyaran kundin tsarin mulkin zai ba hukumar INEC damar gudanar da zaɓe a rana guda
  • Abbas ya ce wannan tsarin zai inganta zabe, rage koma-baya wajen fita kada kuri’a, tare da inganta tsarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya yi magana kan shirin kawo sauyi a tsarin yadda ake gudanar da zabe a Najeriya.

Rt. Hon. Abbas ya bayyana cewa suna duba yiwuwar gyaran kundin tsarin mulki domin a gudanar da dukkan zabubbuka rana guda.

Ana ƙoƙarin sauya tsarin zaben Najeriya gaba daya
Shugaban hukumar zabe, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da kakakin majalisa, Tajudden Abbas. Hoto: House of Representatives, INEC Nigeria.
Source: Facebook

Rahoton TheCable ya ce Abbas ya bayyana haka ne a Abuja yayin taron da ya yi da tawagar Tarayyar Turai, inda ya ce hakan zai karfafa amincin zabe.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji dalilin da ya sa Atiku Abubakar ke jan kafa kan batun takara a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake gudanar da zabe a yanzu

A halin yanzu, ana gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya da suka hada da na wakilai da na sanatoci rana guda.

A tsarin, ana raba zaɓen shugaban kasa da na gwamnoni wanda ake hada zaben gwamna da na majalisun jihohi.

Abin da wasu 'yan kasa ke gani kan zabe

Kwamred Isa Muh'd Makanike daga Gombe ya fadawa Legit Hausa cewa zai yi wahala a samu nasarar yin zaɓe a rana daya.

Ya ce:

"Tabbas idan hakan zai yiwu za a samu sauki amma fa yadda komai ya lalace a kasar nan abin da wahala saboda rashin kayan aiki da cin hanci a tsakanin mutane."

Wasu na ganin neman sauya tsarin zaben zai rage magudi da ake shiryawa musamman a tazarar mako daya da ake bayarwa kafin zaben gwamnoni.

Abin da Tajudden Abbas ya ce kan tsarin

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta fadi irin zaben da shugaba Tinubu ya ke so a 2027

Hon. Abbas ya ce zaben rana guda zai taimaka wurin rage sake fita kada kuri’a, sannan ya tabbatar da cewa majalisar na shirye kan kudurin gyaran kundin tsarin.

Abbas ya kuma bayyana cewa gyaran zai kunshi samar da guraben mata da masu nakasa, da ba sarakunan gargajiya rawar da za su taka a doka.

Shugaban majalisa ya fadi amfanin kudirin sauya tsarin zaben Najeriya
Kakakin majalisar wakilai yayin zamansu a Abuja. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Alkawarin Tajudden ga hukumar zabe

Abbas ya bukaci Tarayyar Turai ta tallafa wajen yada wannan sabon tsari, yana mai jaddada cewa majalisun jihohi suma za su bukaci amincewa da kudurin.

Ya kara da cewa za su yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa hukumar INEC ta samu kayan aiki domin inganta zaben 2027.

A baya, irin wannan yunkuri ya taba samun tsaiko a majalisu da suka gabata, amma yanzu an ce akwai shirin tabbatar da nasarar haka, cewar The Nation.

Tinubu na son ingantaccen zabe - Tajudden Abbas

Mun ba ku labarin cewa shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce Bola Tinubu na da niyyar tabbatar da gaskiya da inganci a zaben 2027.

Majalisar dokoki na aiki kan sauya dokar zabe ta 2022 domin magance matsalolin da aka fuskanta a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: Zuwa kotu da abubuwan da ake fada kan takarar Jonathan a 2027

Rahotanni sun nuna cewa ajudeen Abbas ya yi wannar maganar ne yayin ganawa da shugabannnin EU a Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.