Atiku Ya Yi Magana kan Sahihancin Zaben 2027 da Tawagar Tarayyar Turai
- Atiku Abubakar ya karɓi tawagar Tarayyar Turai (EU) a birnin tarayya Abuja ƙarƙashin jagorancin Barry Andrews
- Rahotanni sun ce ziyarar ta mayar da hankali ne kan bin diddigin shawarwarin da aka bayar bayan zabukan 2023
- Atiku ya jaddada bukatar yin gyaran dokokin zabe kafin 2027 domin tabbatar da ingantaccen tsarin dimokuraɗiyya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan tsarin zabe a Najeriya bayan wata muhimmiyar ganawa da wakilan Tarayyar Turai (EU).
Ganawar, wadda ta gudana a yammacin Alhamis a Abuja, ta haɗa manyan jami’an EU da suka nuna damuwa kan makomar tsarin zaben ƙasar.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Atiku Abubakar ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron Atiku Abubakar da tawagar EU a Abuja
Tawagar Tarayyar Turai ta haɗa da jakadan EU a Najeriya, H.E Gautier Mignot, da kuma Barry Andrews, memban majalisar Turai wanda ya shugabanci tawagar EU-EOM a zabukan 2023.
Sun tattauna kan abubuwan da suka shafi sahihancin zabuka, amincewar ‘yan kasa, da rawar da hukumar INEC ke takawa wajen tabbatar da gaskiya.
Atiku ya bayyana cewa wannan ziyara ta nuna yadda ƙasashen Turai ke da muhimmiyar rawa wajen tallafa wa Najeriya a fannin dimokuraɗiyya.
Ya ce ganawar ta buɗe fagen tattaunawa kan yadda za a tura bukatun jama’a cikin tsarin dokoki da gyare-gyare kafin zabukan 2027.
Shawarwarin EU bayan zaben 2023
Tawagar EU ta gabatar da jerin shawarwari bayan zabukan 2023, inda suka bukaci a samar da dokokin zabe da za su kare kuri’ar jama’a.
Wannan ya haɗa da buƙatar inganta fasahohin amfani da na’urorin BVAS da kuma karfafa matakan tabbatar da gaskiya.
Sai dai Atiku ya nuna damuwa cewa bayan shekara biyu, babu wani alamun da ke nuna INEC na shirin aiwatar da waɗannan gyare-gyare.

Source: Facebook
Ya ce hakan na iya haifar da rashin tabbas a zabukan 2027, abin da zai iya raunana tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.
Kiran Atiku kan gyaran dokokin zabe
Atiku ya yi kira ga majalisar dokoki da hukumar INEC da su hanzarta aiki tare domin samar da dokar zabe mai inganci.
Ya ce yin hakan zai tabbatar da sahihin tsarin da zai bai wa ‘yan ƙasa kwarin gwiwar shiga zabubbuka.
Ya kara da cewa shi da mabiyansa za su ci gaba da goyon bayan ƙungiyoyin farar hula, kungiyoyin kasa da kasa da na cikin gida, musamman EU-EOM, domin inganta zabe.
Tawagar EU ta gana da INEC
A wani rahoton, kun ji cewa tawagar tarayyar turai ta gana da shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Rahotanni sun bayyana cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a inganta zaben Najeriya, musamman na 2027.
Shugaban INEC ya yi kira ga majalisar kasa da ta tabbatar da cewa an gyara dokokin zabe da wuri domin fuskantan 2027 cikin shiri.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

