Makinde: Kusa a PDP Ya Samo Gwamnan da Zai Iya Kifar da Tinubu a 2027

Makinde: Kusa a PDP Ya Samo Gwamnan da Zai Iya Kifar da Tinubu a 2027

  • Kusa a jam'iyyar PDP, Hon. Abiodun Awoleye, ya bayyana wasu halayen gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde
  • Abiodun Awoleye ya bayyana cewa Gwamna Makinde yana da kwarewar da zai iya kifar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
  • Ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnan ya samu wajen jagorantar jihar Oyo tun daga shekarar 2019

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Tsohon ɗan majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar PDP, Hon. Abiodun Awoleye, ya auna gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da Shugaba Bola Tinubu.

Abiodun Awoleye ya bayyana cewa Gwamna Makinde na da karfi a siyasance da kwarewar jagoranci da za su iya taimakawa PDP ta kwato kujerar shugaban kasa daga hannun Shugaba Tinubu a 2027.

Jigo a PDP ya ce Makinde zai iya kifar da Tinubu a 2027
Gwamna Makinde da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @DOlusegun, @SeyiMakinde
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta ce Abiodun Awoleye ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da ‘yan jarida a gidansa da ke Bashorun, Ibadan, yayin bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai.

Kara karanta wannan

Ana bikin murnar 'yancin kai, Akpabio ya yi wa Shugaba Tinubu albishir kan zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me jigon PDP ya ce kan Makinde?

Abiodun Awoleye ya bayyana Gwamna Makinde a matsayin dan siyasa mai tawali’u, abin dogaro wajen tattaro mutane daga tushe, kuma gogaggen mai mulki wanda yake da baiwa ta musamman.

“Gwamna Makinde ya nuna karfin siyasa na musamman da kuma kwarewa wajen gudanar da mulki. Ina da tabbacin cewa yana da abin da ake bukata domin ya daidaita jam’iyyarmu ta PDP kuma ya tabbatar da cewa mun koma kan mulki a matakin kasa.”

- Abiodun Awoleye

Abiodun Awoleye ya kara da cewa nasarar Makinde wajen haɗa kan PDP a jihar Oyo da kuma tafiyar da gwamnati ta hanyar jan kowa a jiki, hujja ce da ke nuna zai iya sake gina PDP a matakin kasa.

An yabawa Gwamna Makinde

Jigon na PDP ya kuma yaba da salon mulkin Makinde, musamman yadda yake biyan albashi, fansho da kuma giratuti ba tare da jinkiri ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya hadu da shugaban kasa, Tinubu ya magantu kan zargin kisan Kiristoci

Ya bayyana cewa hakan ya zama muhimmin abu ga ma'aikata a lokacin da kasar nan ke fuskantar matsin lambar tattalin arziki.

"Ko marigayi Alaafin na Oyo ya taɓa cewa abin mamaki ne yadda Gwamna Makinde ke gudanar da mulki cikin sauki ba tare da ma'aikata sun taɓa biyo shi bashin albashi ko na wata guda ba."

- Hon. Abiodun Awoleye

A cewarsa, yadda Makinde ke biyan ma’aikata albashi da fansho ba tare da tangarda ba ya taimaka sosai wajen samar da kwanciyar hankali da kawo ci gaban tattalin arziki a jihar.

Jigo a PDP ya yabi Gwamna Seyi Makinde
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde. Hoto: @SeyiMakinde
Source: Facebook

Ya bayyana shi a matsayin mutum mai basira, wanda ya kamata a yi nazari kan dabarunsa na mulki domin farfaɗo da kasar nan gaba ɗaya.

A karshe, ya bayyana Makinde a matsayin mutum mai kirkirar hanyoyin warware matsaloli tare da kwarewa wajen warware rikice-rikice.

Hakazalika ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su ci gaba da saka gwamnan a cikin addu’o’insu na yau da kullum.

An goyi bayan tazarcen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar tsofaffin tsageun Neja Delta ta samu matsaya kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Tattali da tsaro,' Bangarori 23 da Tinubu ya tabo a jawabinsa na ranar 'yanci

Kungiyar ta bayyana cewa tana goyon bayan shugaban kasan ya ci gaba da mulkin Najeriya har bayan shekarar 2027.

Ta bayyana cewa yankin Neja Delta ya samu abubuwan more rayuwa masu yawa a shekaru biyun da Tinubu ya kwashe kan mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng