Kwana Ya Kare: Yadda Wani Shugaban APC Ya Mutu Yana cikin Raba N50,000

Kwana Ya Kare: Yadda Wani Shugaban APC Ya Mutu Yana cikin Raba N50,000

  • Mutuwar shugaban APC na mazabar Ukanafun a jihar Akwa Ibom, John Marcus ta haifar da rudani da ce-ce-ku-ce
  • Matar marigayin ta fito ta yi karin haske kan yadda mijinta ya rasu a wurin rabon kudin da wani dan siyasa ya ba su
  • A baya dai wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Marcus ya yi kokarin cinye kudin, lamarin da sauran mambobi suka ki amincewa da shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Matar Shugaban Jam’iyyar APC na mazabar Ukanafun a Jihar Akwa Ibom ta ba da labarin yadda mijinta, John Marcus, ya rasu yayin rabon N50,000.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin 'yan siyasar da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC a mazabar ne suka bayar da wannan kudi ga shugabannnin jam'iyya.

Kara karanta wannan

Ganduje ya hadu da shugaban kasa, Tinubu ya magantu kan zargin kisan Kiristoci

Tutar jam'iyyar APC.
Hoton tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya. Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Getty Images

Marcus, wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na Ukanafun Ward 2, ya rasu a watan Yuni, 2025, kamar yadda Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mene ne ya yi ajalin shugaban na APC?

APC ta mazabar Ukanafun, ta bakin mai magana da yawunta, Stanley Peter, ta bayyana mamaki kan rasuwar Marcus, inda ta kira shi da "jajirtaccen shugaba mai kishin jam’iyya.”

“Marigayin, wanda ya kasance jagora mai kishi da jajircewa, ya rasu ba tare da wata alamar rashin lafiya ba,” in ji sanarwar da APC ta fitar a ranar 26 ga Yuni.

Sai dai bayan kwana uku, jaridar The Sun ta ruwaito cewa Marcus ya mutu ne a wata arangama da wasu mambobin PDP da suka ki bin Gwamna Umo Eno zuwa APC.

Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa:

“Rikici ya barke ne lokacin da wani ɗan siyasa a mazabar, wanda ya sauya sheka zuwa APC, ya ba shugabanni kuɗi. Amma shugaban APC na mazabar ya nemi cinye kudin, sai mambobi suka ki amincewa, fada ya kaure har aka kashe shi.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 da ya kamata jam'iyyar ADC ta yi don kayar da Tinubu, APC a zaben 2027

Sai dai wannan bayanin bai yi wa APC reshen mazabar Ukanafun daɗi ba. Mai magana da yawun jam’iyyar, Peter, ya fito ya karyata rahoton jaridar.

Matar marigayin ta fadi abin da ya faru

A cikin hirar da ta yi da Premium Times makon da ya gabata, matar marigayi Marcus ta bayyana cewa labarin da aka wallafa a jarida ba gaskiya ba ne.

Ta ce mijinta ya fadi ne daga kujerarsa yayin rabon N50,000 da masu sauya sheka daga PDP suka ba shi.

Ta ƙaryata zargin tashin hankali ko fada, tana mai cewa: “Babu wani fada. Mutanen da suka halarta sun shaida cewa bayan ya fara rabon kuɗin, sai kawai ya fado daga kujerarsa.”

Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom.
Hoton Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom a wurin ibada. Hoto: Pastor Umo Eno
Source: Facebook

A cewarta, shugabannin APC na mazabar ne kaɗai aka gayyata a wurin, babu mambobin PDP, kuma yayin rabon kuɗin ne wani ya tsoma baki ya nemi a haɗa da matasa.

"Daga nan mijina ya ci gaba da rabon kuɗin. Bayan ya ba mutane biyu kuɗi, sai kawai ya fadi daga kujerarsa.”

Ta ce wannan ne ainihin abin da ya faru, babu wani abu dabam, sai dai ta tabbatar da cewa babu wani ciwo da ke damun mijinta.

Kara karanta wannan

'Yan Kwankwasiyya sun rabu da Kwankwaso da Abba, sun hade da Barau a APC

An yabi Gwamna Eno da ya koma APC

A wani labarin, kun ji cewa Wike ya yabawa Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom bisa matakin da ya dauka na sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Ministan Abuja ya yi wannan yabo ne a ranar Laraba yayin kaddamar da titin Ikot Esu–Otomo–Azumini mai tsawon kilomita 15.13 a Akwa Ibom.

Ya ce hadewar Gwamna Eno da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a inuwa data, za ta kawo ƙarin ayyukan ci gaba ga jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262