Abubuwa 4 da Ya Kamata Jam'iyyar ADC Ta Yi don Kayar da Tinubu, APC a Zaben 2027

Abubuwa 4 da Ya Kamata Jam'iyyar ADC Ta Yi don Kayar da Tinubu, APC a Zaben 2027

Abuja - Jam’iyyar ADC ta zama sabuwar mafita ga shugabannin adawa da ke shirin haduwa domin kifar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya fara wannan yunkuri inda ya bukaci shugabannin adawa su hada karfi da karfe a zaben mai zuwa.

An bukaci ADC da ta kiyaye abubuwa 4 domin lashe zaben shugaban kasa a 2027
Hoton Shugaba Bola Tinubu da tambarin ADC da Alhaji Atiku Abubakar. Hoto: @tinubu, @atiku
Source: Twitter

Daga bisani, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, da kuma Rotimi Amaechi, da wasu kusoshin adawa, suka hadu a karkashin ADC don kifar da Tinubu, inji rahoton Punch.

Sai dai kafin jam’iyyar ta cimma burinta na kifar da gwamnatin Tinubu, akwai wasu abubuwa guda hudu da ya kamata ADC ta yi su:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Matsalar rabuwar kai a ADC

Atiku, Obi da Amaechi sun nuna sha’awar tsayawa takara a karkashin jam’iyyar, lamarin da ya riga ya jawo barakar cikin gida.

Kara karanta wannan

Tazarce: An zakulo manyan abubuwa 6 da za su taimaka wa Tinubu ya ci zabe a 2027

Kamar yadda ya faru da PDP a 2023, babu jam’iyyar da za ta shiga zabe, kuma ta yi nasara, alhalin gidanta a rabe yake - babu hadin kai.

Idan ADC na son kifar da gwamnatin Bola Tinubu, to lallai akwai bukatar ta hada kan 'ya'yanta musamman masu son yin takara.

2. Rabon kujeru na shugabanci

Na biyu shi ne batun rabon kujeru. PDP ta fada irin wannan matsalar a 2023 lokacin da ta bude tikitin shugaban kasa ga kowa, daga bisani Atiku ya samu nasara, abin da ya kawo rikici a jam’iyyar.

Magoya bayan Obi sun nuna damuwarsu kan batun rabon kujeru idan zaben 2027 ya zo, bayan jagororin ADC sun bukaci su sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Ana fargabar, idan ADC ta yi kuskuren yin watsi da kiran Kudu na shugabancin kasa, hakan na iya lalata burinta na zama jam'iyya mai mulki daga 2027.

3. Kokarin jawo Goodluck Jonathan

Na uku shi ne, jam'iyyar ta yi wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tayin shiga tafiyar hadakar 'yan adawa.

Ana ganin Jonathan zai yi wa'adi daya ne kacal idan ya hau mulki, kuma wannan zai sa ya kammala wa’adin kudu na yin mulki shekara takwas.

Kara karanta wannan

Atiku ya shirya hakura da takara da Tinubu a 2027? An ji gaskiyar zance

Sai dai wasu na ganin ya kamata ya zauna a matsayin dattijo, mai fada a ji, maimakon komawa siyasa, inji rahoton Vanguard.

Masani kan harkokin siyasa, Omotayo Yusuf, ya bayyana wa Legit.ng cewa:

“Zai fi kyau Jonathan ya yi ritaya daga siyasa, ya zama dattijon kasa, maimakon sake shiga takara.”
Ana ganin jam'iyyar ADC za ta iya kayar da Tinubu a 2027 idan ta hada kai da Jonathan
Dama zuwa Hagu: Malam Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, Atiku Abubakar, David Mark, Rau'uf Aregbesola, a taron kaddamar da ADC a Abuja. Hoto: @atiku
Source: Facebook

4. Bukatar tsare-tsare masu ma’ana

Na hudu kuma shi ne bukatar ADC ta bayyana tsare-tsarenta ga al’ummar Najeriya, ganin cewa zaben 2027 na gabatowa.

A yanzu, abin da aka fi jin ta bakinta shi ne cewa 'gwamnati ta Tinubu ta gaza,' amma har yanzu ba ta fayyace yadda za ta magance matsalar tsaro, tattalin arziki da sauran matsaloli ba.

Wannan batu na da matukar muhimmanci tunda yawancin manyan shugabannin jam’iyyar sun taba rike madafun iko a lokacin da matsalolin kasar suka tsananta kafin APC ta hau mulki.

'Mu ne da nasara a 2027' - Surajo Caps

Alhaji Surajo Caps, fitaccen matashin dan jam'iyyar PDP, a zantawarsa da Legit Hausa, ya ce yana da yakinin cewa hadakarsu Atiku Abubakar ce za ta samu nasara a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Yadda wani shugaban APC ya mutu yana cikin raba N50,000

Surajo Caps ya ce:

"Mu duk inda Atiku ya ke muna tare da shi, kuma har a cikin mafarkinmu muna ganin nasararmu a 2027.
"Ba na tunanin akwai wani shiri da tsagin adawa suka taba yi da ya kai wanda hadakar ADC ke yi yanzu, ko APC ba za ta kai ta karfi ba."

Surajo Caps ya ce akwai bukatar masu kishin Najeriya su fito su marawa hadakarsu Atiku baya, domin ceto kasar nan daga halin da take ciki yanzu.

ADC ta gargadi Atiku gabanin 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar ADC ta gargadi Alhaji Atiku Abubakar da sauran jiga-jigan 'yan siyasa kan mallakar katin dan jam'iyya.

Shugaban ADC, reshen jihar Adamawa ya ce dole ne manyan ‘yan siyasa su yi rijista a mazabunsu kafin karshen shekarar nan don tunkarar 2027.

Shehu Yohanna ya gargadi Atiku da Babachir Lawal cewa ba za su iya rike mukami ko yanke shawara a madadin jam'iyyar ba ma damar ba su da rajista.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com