An Fara Tada Jijiyoyin Wuya a PDP da Gwamna Ya Nuna Alamun Zai Sauya Sheka zuwa APC

An Fara Tada Jijiyoyin Wuya a PDP da Gwamna Ya Nuna Alamun Zai Sauya Sheka zuwa APC

  • Jiga-jigan PDP sun fara nuna damuwarsu kan jita-jitar da ke nuna Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu zai koma APC mai mulkin Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP reshen Enugu, Cif Augustine Nnamani ya dora laifin duk matakin da Gwamna Mbah ya dauka kan jam'iyyar PDP
  • Ya kuma tabbatar da cewa Gwamna Mbah na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin yanke hukuncin karshe kan yiwuwar barin PDP

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Tsohon Shugaban PDP a jihar Enugu, Cif Augustine Nnamani, ya nuna bacin ransa kan yadda jam'iyyar ke neman ta kori Gwamna Peter Mbah.

Nnamani ya bayyana cewa idan har Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya koma APC, babu wanda ya jawo hakan face PDP.

Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu.
Hoton Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu Hoto: Peter Mbah
Source: Twitter

Vanguard ta ce rahotanni sun dade suna yawo cewa Gwamna Mbah na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir ya aika da muhimmin sako ga jami'an gwamnatinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jita-jitar sauya shekar Gwamna Mbah ta yi karfi

A makon jiya, wasu majiyoyi masu karfi suna tabbatar wa Premium Times cewa Gwamna Mbah zai sanar da lokacin shiga APC bayan kammala wasu shirye-shirye.

Rahoton ya nuna cewa tsofaffin gwamnonin Enugu, ciki har da Sullivan Chime da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ken Nnamani, sun taka rawa wajen jawo ra'ayin Gwamna Mbah zuwa APC.

Sai dai mai magana da yawun gwamnan, Uche Anichukwu, ya tabbatar da cewa an yi taruka a jihar kan lamuran siyasa, amma ya musanta batun yanke hukuncin barin PDP.

Laifin waye idan gwamnan ya koma APC?

Amma a martaninsa ranar Litinin, Cif Augustine Nnamani ya ce ba zai yi mamaki ba idan Mbah ya koma APC ko wata jam’iyya, yana mai cewa PDP ce ya kamata ta dauki alhakin hakan idan ya faru.

“Eh, ina tabbatar muku cewa ana tattaunawa kan makomar Jihar Enugu da kuma yankin Kudu maso Gabas baki ɗaya, ganin yadda PDP ta yi wa yankin.

Kara karanta wannan

Ganduje ya taso Gwamna Abba a gaba, ya fadi kuskuren da yake yi a gwamnatinsa

"Amma hukuncin karshe na hannunmai girma gwamna, kuma zai dauki mataki ne bisa abin da ya samu daga shawarwarin da yake yi.
“A matsayina na mai kishin PDP, abin takaici ne yadda aka bar abubuwa suka tabarbare a cikin jam’iyyar," in ji shi.

Mene ne ya fusata Gwamna Mbah a PDP?

Ya tuna yadda PDP ta Kudu maso Gabas ta bi umarnin uwar jam'iyya ta kasa wajen mika sunan Hon. Sunday Udeh-Okoye domin ya maye gurbin sakataren jam'iyya.

Ya nuna takaicinsa kan yadda PDP ta yi watsi da zabin Kudu maso Kudu, ta dawo da Sanata Samuel Anyanwu duk da ya bar mukamin lokacin da ya nemi takarar gwamnan a Imo.

Gwamnan Enugu, Peter Mbah.
Hoton Gwamna Peter Mbah yana dagawa jama'a hannu a jihar Enugu Hoto: Peter Mbah
Source: Facebook

Augustine Nnamani ya zargi jam’iyyar da cin amanar Gwamna Mbah da kuma PDP ta Kudu maso Gabas.

Ya kara da cewa idan ta tabbata Gwamna Mbah ya bar PDP, to jam'iyyar ta rasa yankin da take da karfi tun 1999.

Shirin Gwamna Mbah ya fara rikita APC

A wani labarin, kun ji cewa an fara tayar da jijiyoyin wuya a APC kan jita-jitar da ke nuna Gwamna Peter Mbah na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an kara samun gwamnan PDP da zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Wasu jiga-jigan APC sun zargi Ministan Kimiyya da Fasaha da kokarin hana gwamnan shigowa jam'iyyar, inda suka ce ba za su lamunci hakan ba.

Sun bayyana cewa matukar ministan ya ci gaba da yunkurin hana Gwamna Mbah shiga APC, za su tafi Abuja su nemi a tsige shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262