PDP Ta Raba Gardama kan Batun Zaman Jonathan Mamba a Jam'iyyar
- Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya watau PDP, ta yi magana kan kasancewar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, daya daga cikin mambobinta
- PDP ta bayyana cewa har ya zuwa wannan lokaci, tana tare da Jonathan wanda ake hasashen zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027
- Hakasalika, jam'iyyar ta yi watsi da batun rarrabuwar kai sakamakon zaben shugabanninta da aka gudanar a jihar Cross Rivers
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta yi magana kan zaman tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, mamba a cikinta.
PDP ta bayyana cewa har yanzu Goodluck Jonathan mamba ne na jam’iyyar.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 29 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Debo Ologunagba ya yi bayanin ne yayin taron manema labarai kan shirin PDP na gudanar da babban taronta na kasa a watan Nuwamba.

Kara karanta wannan
"Sai an je gaban kotu," Fadar shugaban kasa ta kara tabo batun takarar Jonathan a 2027
Me PDP ta ce kan Goodluck Jonathan?
Ya yi bayanin ne a matsayin martani ga ikirarin tsohon ministan yada labarai kuma jigon PDP, Farfesa Jerry Gana, wanda ya ce Jonathan zai tsaya takarar shugabancin kaa a 2027 a karkashin PDP kuma zai yi nasara.
Jonathan, wanda PDP ke kokarin dawo da shi cikin harkokin jam’iyyar, bai cika halartar tarurrukan PDP ba tun daga shekarar 2016 lokacin da jam’iyyar ta shiga rikici bayan faduwar zaɓen 2015.
Da aka tambaye shi kan maganar Jerry Gana, sai Ologunagba ya kada baki ya ce:
“Ba ni ne mai magana da yawun Farfesa Jerry Gana ba. Kowa na da ’yancin faɗin ra’ayinsa. Amma zan jaddada wannan, a jam’iyyar nan, kamar yadda muke a yau, Shugaba Jonathan mamba ne, bai taɓa cewa ba mamba ba ne.”
Sai dai, Ologunagba ya ce PDP na da ’yan Najeriya da suka cancanta sosai, musamman daga cikin gwamnoni, waɗanda suka yi kyakkyawan aiki kuma za su iya samun goyon bayan ’yan kasa don su yi hakan a matakin kasa.
"Bisa girmamawa ba ni ne mai magana da yawun Jonathan ba, haka kuma ba ni ne mai magana da yawun Jerry Gana ba. Amma jam’iyyarmu ta mayar da hankali kan babban taronmu."
- Debo Ologunagba
PDP ta musanta batun rikici a jam'iyyar
Ologunagba ya kuma musanta jita-jitar cewa rikici ya taso a jam’iyyar game da zaben shugabannin PDP da aka shirya a jihar Cross River, rahoton The Punch ya tabbatar da labarin.
Ya kuma yi martani kan wasikun da suka ci karo da juna na shugaban PDP na kasa, Iliya Damagum, da sakataren jam’iyya na kasa, Samuel Anyanwu, wadanda suka aikawa hukumar INEC game da zaben shugabannin.

Source: Twitter
"Bari in faɗa muku a fili. Babu rikici a nan. Zan iya gaya muku da tabbaci cewa NWC ta haɗu wuri guda a kan wannan batu. Mun amince baki ɗaya cewa a dage zaben saboda dalilan da na riga na bayyana.”
"Saboda haka ba zan yi magana sosai kan wannan batu ba, saboda abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa babu wani zaben shugabanni da aka gudanar a can.”
- Debo Ologunagba
Jonathan ya fadi halinsa kan yafiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa bai da riko ko kadan a zuciyarsa.
Jonathan ya bayyana cewa bai taba kullatar kowa ba a zuciyarsa kan laifuffukan da aka taba yi masa a baya.
Tsohon shugaban kasan ya yi kira ga shugabanni kan su koyi halin yafiya domin samun ci gaba da hadin kai a kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

