2027: Kusa a APC Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Hango Yadda APC Za Ta Lashe Zabe a Kano
- Wani kusa a jam'iyyar APC a jihar Kano, ya hango ya hango yadda za su samu nasara a babban zaben shekarar 2027
- Hon. Seyi Olorunsola ya bayyana cewa APC za ta yi nasara ba tare da goyon bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Ya nuna cewa ya kamata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban APC na kasa, su daina daukar Kwankwaso da wani muhimmanci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Wani kusa a jam’iyyar APC a jihar Kano, Hon. Seyi Olorunsola, ya yi magana kan yiwuwar lashe Kano ba tare da goyon bayan Rabiu Musa Kwankwaso ba.
Hon. Seyi Olorunsola ya bayyana cewa jam’iyyar za ta samu nasarar kawo Kano ga Shugaba Bola Tinubu, ɗan takarar gwamna, da sauran ‘yan takarar APC ba tare da hadin kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa Hon. Seyi Olorunsola, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai a Kano ranar Lahadi, 28 ga watan Satumban 2025.
Me kusa a APC ya ce kan Kwankwaso?
Olorunsola, wanda shi ne shugaban kungiyar Tinubu/Barau/Atah Movement, ya ce Shugaba Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, suna tankawa Kwankwaso fiye da kima.
Ya ce mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, karamin ministan gidaje, Yusuf Abdullahi Atah, da Sanata Kawu Sumaila suna da isasshen karfin siyasa da zai tabbatar da nasarar APC a Kano a 2027.
Yadda APC za ta yi nasara a Kano
Kusan na APC ya ce Atah daga Kano ta Tsakiya zai iya tinkarar Gwamna Abba Kabir Yusuf, Barau Jibrin da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje suna da tasiri a Kano ta Arewa, yayin da Sumaila ke da magoya baya a Kano ta Kudu.
Ya kuma bayyana cewa kungiyar Tinubu/Barau/Atah Movement ta amince da Barau Jibrin a matsayin ɗan takarar gwamna na 2027, tare da Yusuf Abdullahi Atah a matsayin mataimakinsa, rahoton New Telegraph ya tabbatar da labarin.
"Kwankwaso ya san da wannan tsari, kuma yana tsoron yadda farin jinin Barau ke karuwa a jihar; shi ya sa yake neman shiga APC domin tarwatsa wannan tsari da kuma tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf."
"A 2019, mun doke shi lokacin da ya tsayar da Abba Kabir Yusuf a karkashin PDP."
"A 2023 kuma, mun lashe zaɓen gwamna a runfuna, mun yi nasara a kotun sauraron korafe-korafen zaɓe; mun lashe a kotun daukaka kara, amma Kotun Koli ta yi hukunci wanda bai mana dadi ba."
"Kowa ya sani Kwankwaso ba ɗan NNPP ba ne, don haka ba shi da ikon yin magana ko yarjejeniya a madadin jam’iyyar da ba ya cikinta."
"Bai kamata Shugaba Tinubu ya dogara da Kwankwaso a matsayin wanda zai kawo masa nasara a Kano ba."
"Ba zai yiwu Kwankwaso ya shigo APC kawai saboda ya yi magana da shugaban kasa ko shugaban jam’iyya ba. Mun san irin kalaman da ya taɓa yi kan Shugaba Tinubu da Ganduje."
- Hon. Seyi Olorunsola

Source: Twitter
Ganduje ya soki Gwamna Abba Kabir
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya soki magajinsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ganduje ya yi zargin cewa Gwamna Abba ya samu kudade daga asusun tarayya cikin watanni shida, fiye da wanda ya samu a shekara takwas.
Tsohon gwamnan ya nuna cewa gwamnatin Gwamna Abba ba ta san yadda ake gudanar da harkokin mulki ba, kuma ba ta sa komai a gaba ba sai ramuwar gayya.
Asali: Legit.ng


