Ganduje Ya Hada Kwankwaso, Abba Kabir Wuri Guda, Ya Musu Wankin Babban Bargo

Ganduje Ya Hada Kwankwaso, Abba Kabir Wuri Guda, Ya Musu Wankin Babban Bargo

  • Tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki Sanata Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusfu
  • Ganduje ya koka da salon mulkin NNPP a Kano inda ya kira siyasar su rashin daidaito da gwamnatin rashin tabbas
  • A taron shugabannin APC a Kano, Ganduje ya ce Kwankwaso ba shi da tsayayyen matsayi, yana yiwa jam’iyya izgili, yanzu kuma yana neman dawowa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Yusuf.

Ganduje ya bayyana takaici yadda suke gudanar da mulki a jihar yana kiran siyasar su da ta rashin tabbas da bita da kulli.

Gnaduje ya dura kan Abba Kabir da mai gidansa, Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Abba Kabir da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Ganduje ya dura kan Kwankwaso, Abba Kabir

Tsohon gwamann Kano ya bayyana haka a wani hira da BBC Hausa inda ya tabo batutuwa da dama game da siyasarsa.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso zai yi alaka da Ganduje idan ya koma APC da wasu abubuwa 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A taron shugabannin APC da aka yi a Kano, Ganduje ya ce Kwankwaso ya daɗe yana izgili ga APC, yanzu kuma ana rade-radin dawowarsa.

Ya ce:

“Mun ji jita-jita amma ba mu ɗauke su da muhimmanci ba, Kwankwaso ya taɓa cewa mahaukaci ne kawai zai shiga APC.”

Game da yiwuwar sulhu da Kwankwaso da Shekarau, Ganduje ya ce hakan ba matsala ba ce, saboda dukansu suna da gogewar mulki da zai taimaka.

Ganduje ya jaddada cewa gwamnatin Gwamna Abba Yusuf ta fara ne da bincike, amma duk da kuɗaɗen da aka samu, ba a iya fitar da wani abin a zo a gani ba.

Ya kara da cewa:

“Wannan gwamnati ba ta da cikakken hangen nesa. Gwamnatinsu ce ta ramuwar gayya, tana kashe kuɗi akan ayyuka ba tare da ba su dace ba.”
Ganduje ya magantu kan cire shi a shugaban APC
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

Ganduje ya magantu kan murabus a shugabancin APC

Kan murabus a matsayin shugaban APC na ƙasa, Ganduje ya ce rabon siyasa ne kawai, ba don rashin adalcin shugaban ƙasa Bola Tinubu ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan Kwankwaso, Ganduje ya ragargaji Abba, ya fadi kuskuren gwamnan Kano

Tsohon gwamnan Kano ya ce ya ce hakan ba matsala ba ne kawai an yi ne saboda maslahar siyasa da kuma duba sauran yankuna game da shugabancin jam'iyyar.

Ya ce:

"Shugaban ƙasa bai yi min wani abu ba. Mulki nufin Allah ne; yana ba wa wanda ya so, a lokacin da ya ga dama."

Ganduje ya ƙaryata ikirarin cewa APC tana rugujewa, inda ya jaddada cewa duk da ficewar wasu, jam’iyyar mai mulki ita ce babba a Najeriya.

Har zuwa lokacin kammala rahoton nan, Kwankwaso, ko kuma Gwamna Abba Yusuf ba su mayar da martani ga caccakar Ganduje ba.

APC ta magantu kan komawar Kwankwaso cikinta

Kun ji cewa mai magana da yawun APC a jihar Kano ya ce jam’iyyar ba ta bukatar dawowar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun bayyana cewa ya yi watsi da ikirarin Sanata Kwankwaso na cewa shi ne ya assasa APC a Kano.

A daya bangaren kuma, jigo a NNPP, Buba Galadima ya ce an yi wa maganganun Kwankwaso fassara maras kyau.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com