Tsugunne Ba Ta Kare ba": Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar PDP
- Rigima ta sake kunno kai a babbar jam'iyyar PDP ami adawa a Najeriya kan zabubbukan shugabanni a wasu jihohi guda uku
- Shugaban jam'iyyar na kasa, Umar Iliya Damagum, ya sanar da dage zabubbukan inda ya kawo dalilan daukar wannan mataki
- Sai dai, sakataren PDP na kasa ya kekasa kasa ya ce ko kadan ba haka ba ne kuma za a gudanar da zabubbukan kamar yadda aka shirya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Rikici ya sake kunno kai a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya kan zaben shugabanni.
Rikicin ya taso ne tsakanin bangarori biyu na jam’iyyar PDP kan gudanar da zabubbukan shugabanni a jihohin Cross River, Plateau da Kebbi.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa bangarorin biyu sun bada mabambantan bayanai kan zabubbukan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban jam'iyyar PDP ya fitar da sanarwa
A cikin wata wasika dauke da kwanan watan 25 ga watan Satumba, shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Damagum, ya sanar da dage zabubbukan da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 27 ga Satumba 2025.
Ya ce dage zabubbukan ya biyo bayan wasu a'lamura da ba a yi zato ba da kuma kalubale wajen samar da kayan aiki.
"Wannan yana nufin cewa zabubbukan jihohi a jihohin da aka ambata ba za su gudana ba kamar yadda aka tsara tun farko. Za mu sanar da hukumar INEC sabon lokaci idan an kayyade."
- Umar Damagum
Sakataren PDP ya musanta matsayar Damagum
Sai dai kuma, a wata wasika daban dauke da kwanan watan 26 ga Satumba, sakataren jam'iyyar na kasa, Samuel Anyanwu, ya dage cewa za a gudanar da zabubbukan kamar yadda aka tsara tun farko.
Ya ce duk wata sanarwa zuwa ga INEC dole ne ta kunshi sa hannun shugaban jam’iyya na kasa da sakataren jam'iyya na kasa a tare.
"Zabubbukan jihohi a wuraren da aka ambata za su gudana kamar yadda aka tsara. Hukumar INEC ba za ta karɓi kowace wasika ba idan babu sa hannun shugaban jam'iyya na kasa da sakatare a tare."
- Samuel Anyanwu
PDP na fama da rikice-rikicen cikin gida
Wannan sabanin ya sake bayyana rarrabuwar kawuna a shugabancin jam’iyyar PDP.
Tun da farko, jam’iyyar ta shiga rikici kan wanda ya fi cancanta ya rike kujerar sakatare na kasa, tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Udeh-Okoye.

Source: Facebook
A watan Maris, Kotun Koli ta soke hukuncin da ya tsige Anyanwu daga matsayin sakataren PDP na kasa.
Bayan haka ne Damagum ya umarce shi da ya koma bakin aiki, yana mai cewa yanke hukuncin dawo da shi a matsayin sakatare ya kasance mai wahala.
Samuel Anyanwu dai na daya daga cikin na hannun daman ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Gwamnan PDP zai koma jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya shirya sauya sheka daga jam'iyyar PDP.
Alamu sun nuna cewa gwamnan ya shirya koma jam'iyyar APC mai mulki, idan har ba wani sauyi aka samu ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa Gwamna Peter Mbah ya kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan shirinsa na komawa APC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


