Magoya Bayan Peter Obi Sun Tanka bayan ADC Ta Ba 'Yan Hadaka Umarni

Magoya Bayan Peter Obi Sun Tanka bayan ADC Ta Ba 'Yan Hadaka Umarni

  • Kungiyar magoya bayan Peter Obi wadda aka fi sani da Obidient Movement, ta yi wa jam'iyyar ADC martani game da umarnin ta
  • Shugaban kungiyar na kasa, Yunusa Tanko, ya bayyana cewa sun yi mamakin umarnin da ADC ta ba 'yan hadaka kan su yi murabus daga jam'iyyunsu
  • Yunusa Tanko ya bayyana cewa mai gidansu yana yin shawarwari kafin ya yanke hukunci a harkokin siyasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar Obidient Movement ta magoya bayan Peter Obi, ta yi martani kan umarnin da jam’iyyar ADC ta bayar ga 'yan hadaka.

ADC dai ta bukaci 'yan hadakar da su yi murabus daga tsofaffin jam’iyyunsu domin maida hankali kan jam'iyyar.

Magoya bayan Peter Obi sun yi wa ADC martani
Hoton tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Facebook

Martanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Yunusa Tanko, ya fitar a shafin X a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

ADC ko ADA: 'Yan hadaka sun kammala zabar jam'iyyar da za su yi takara a 2027

'Yan Obidients sun yi martani ga ADC

A cikin sanarwar, Yunusa Tanko ya ce Peter Obi ya riga ya daidaita da matsayar hadaka wajen amincewa da ADC.

Ya jaddada cewa wannan daidaituwar ta shafi zaɓen gwamna na 8 ga Nuwamban 2025 a Anambra da kuma zaɓen shugaban kasa na 2027.

“Mun lura da sanarwar da ADC ta fitar game da matsayar hadaka da rawar da muke takawa a cikinta."
"Wannan matsaya da sanarwa an bayyana su a fili a bainar jama’a, don haka muna mamakin dalilin da yasa ake canza yarjejeniya a tsakiyar tafiya.”

- Yunusa Tanko

Damuwar magoya bayan Obi kan ADC

Yunusa Tanko ya kara da cewa Peter Obi yana yin shawarwari a harkokin siyasa, kuma ya yi hakan ya shiga hadaka, kuma zai yi hakan kafin ya amsa kowane irin wa'adi da aka ba shi.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda ADC za ta tsara tikitin takarar shugaban kasa, yana mai jaddada cewa dole ne a yi adalci da daidaito domin yanzu shugabancin kasa na hannun Kudu.

Kara karanta wannan

'Najeriya ba Legas ba ce,' ADC ta fadi abin da ke shirin faruwa da Tinubu a 2027

“A matsayinmu na Obidient Movement, kasancewar mu cikin manyan wadanda ake shawara da su, mun damu matuka kan yadda jam’iyyar za ta tsara tsarin tikitin shugaban kasa."
"Tunda shugabancin kasa yanzu yana hannun Kudu, dole a yi la’akari da adalci da daidaito idan jam’iyyar na da niyyar samun nasara a zaɓen 2027."

- Yunusa Tanko

Peter Obi zai yi shawara kafin sauya sheka
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Peter Obi bai gaggawar zama shugaban kasa

Yunusa Tanko ya ce Obi ba ya gaggawar zama shugaban kasa, amma babban burinsa shi ne gina Najeriyar da ke aiki ta hanyar magance talauci, inganta tattalin arziki, gyara harkokin lafiya, ilimi da tsaro.

"Waɗannan sune dalilan da suka sa ya shiga hadakar tun farko, dukkansu suna kan kyakkyawan shugabanci, wanda shi ne ginshikin tafiyar Obidient Movement."

- Yunusa Tanko

Obi ya nuna yatsa ga gwamnatin Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya koka kan yadda dimokuradiyya ke samun koma baya a Najeriya.

Peter Obi ya bayyana cewa a yanzu dimokuradiyya ta daina amfanar jama'a, kuma shugabanni suna yin abin da su ke so.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka

Tsohon dan takarar shugaban kasan ya cewa dimokuradiyya na mutuwa a Najeriya, saboda rashin adalci da rashin tallafa wa talakawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng