Siyasar Kano: APC Ta Yi Watsi da Sharadin Kwankwaso na Sauya Sheka
- Mai magana da yawun APC a jihar Kano ya ce jam’iyyar ba ta bukatar dawowar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Rahotanni sun bayyana cewa ya yi watsi da ikirarin Sanata Kwankwaso na cewa shi ne ya assasa APC a Kano
- A daya bangaren kuma, jigo a NNPP, Buba Galadima ya ce an yi wa maganganun Kwankwaso fassara maras kyau
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta yi watsi da sharuddan da aka ce jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kafa kan yiwuwar sauya shekarsa.
Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Ahmed Aruwa, ya bayyana cewa maganganun Kwankwaso ba gaskiya ba ne, kuma ba abin da jam’iyyar ta amince da shi.

Source: Facebook
Yayin tattaunawa da Punch, Aruwa ya ce APC ba ta nemi Kwankwaso ya dawo cikin jam’iyyar ba, balle har ta amince da wasu sharudda daga gare shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin yiwuwar Kwankwaso ya sake shiga APC kafin babban zabe na 2027.
Wane ne ya kafa a APC a jihar Kano?
Mai magana da yawun APC a Kano ya yi fatali da ikirarin Kwankwaso cewa yana daga cikin mutanen da suka assasa jam’iyyar a jihar.
Ya ce gaskiyar magana ita ce tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau ne ya jagoranci kafa APC a Kano, ba Kwankwaso ba.
Haka kuma, Aruwa ya yi jaddada cewa APC ta yi nasara a zaben 2019 ba tare da taimakon Kwankwaso ba, kuma tana da kwarin gwiwar sake cin nasara a 2027.

Source: Facebook
Ya ce ko a lokacin da Kwankwaso ya shiga APC a baya, hakan ya kasance ne da wasu sharuda da aka shimfiɗa masa, kuma akwai hujjoji na wannan batu da za a bayyana idan lokaci ya yi.
Me Kwankwaso ke so a jam'iyyar APC?
Dangane da rade-radin cewa Kwankwaso yana neman damar mallakkar tikitin takarar gwamna a Kano a madadin dawowarsa, Aruwa ya bayyana maganar a matsayin abin dariya.
Ya ce APC a Kano ta riga ta cika da jiga-jigan masu neman takara irin su Sanata Barau Jibrin, tsohon mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna, da kuma A. A. Zaura.
Martanin Injiniya Buba Galadima ga APC
Sai dai a martani, jigon NNPP, Buba Galadima, ya musanta cewa Rabiu Kwankwaso na da shirin komawa APC.
Ya ce an fassara maganganunsa ba daidai ba, inda ya bayyana cewa babu wanda zai koyawa Kwankwaso siyasa.
Ya ƙara da cewa idan har lokaci ya yi da Kwankwaso zai dawo, shi da kansa zai bayyana sharudan, amma yanzu ba lokacin yin hakan ba ne.
Ganduje ya magantu kan Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan sauya shekar Rabiu Kwankaso.
Ganduje ya ce ya ji labarin cewa Rabiu Kwankwaso zai koma APC amma bai dauki maganar da muhimmanci ba.
Ya kara da cewa duk da abin da Kwankwaso ya fada a baya, za su karbe shi idan ya cika sharudan da ake bukata daga gare shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


