Jam'iyyar APC Ta Sake Ruguza 'Yan Adawa, Ta Kara Yawan Sanatoci a Majalisar Dattawa
- Jam'iyyar APC ta samu karin mamba a Majaliiisar Dattawan Najeriya kafin a buga gangar siyasar babban zaben 2027
- Sanatan Enugu ta Gabas, Kelvin Chukwu ya sanar da cewa ya raba gari da jam'iyyar LP, kuma ya koma APC mai mulkin Najeriya
- Ya ce ya yanke shawarar fita daga LP ne saboda rikicin cikin gida da ya dabaibaye ta wanda ya kai ga rabewar jam'iyyar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Sanata mai wakiltar jihar Enugu ta Gabas, Sanata Kelvin Chukwu ya tattara kayansa da magoya bayansa, ya fice daga LP zuwa jam'iyyar APC.
Sanata Kelvin Chukwu ya tabbatar da sauya shekarsa daga jam'iyyar LP zuwa APC mai mulkin Najeriya a jiya Laraba, 24 ga watan Satumba, 2025.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Sanata Chukwu, ya fito ne daga kauyen Amuri da ke cikin karamar hukumar Nkanu ta Yamma a jihar Enugu.
Sanata Chukwu ya halarci taron mazaba
Ya bayyana cewa ya bar LP tare da shiga APC a wurin taron tattaunawa da mutanen mazabarsa da aka gudanar a kasuwar garinsu, ranar Laraba.
A taron, Sanatan ya tunawa al'ummarsa wasu daga cikin nasarorin da ya samu tun daga lokacin da suka tura shi ya wakilce su a Majalisar Dattawa.
Dalilin sanatan na ficewa daga LP zuwa APC
Dan majalisar ya shaida wa mahalarta taron cewa ya yanke shawarar barin jam'iyyar LP ne saboda rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar, wanda ya raba ta gida biyu ko ma a ce uku.
Ya kuma nuna cewa wannan matsalar ta shafi mambobin jam’iyyar sosai, ya na mai ƙara wa da cewa ita ma jam'iyyar PDP na cikin mummunan rikici a halin yanzu.
Sanatan ya bayyana cewa zai sanar da sauya shekarsa zuwa APC a hukumance a zauren majalisar dattawa lokacin da ‘yan majalisar suka koma zama bayan karewar hutu.
Sanata Chikwu ya godewa magoya baya
Sanata Chukwu ya mika godiya ga jama’arsa bisa goyon bayan da suka ba shi tun lokacin da ya hau kujerar dan majalisar tarayya, tare da alkawarin ci gaba da kare muradunsu.
Jaridar Guardian ta ce taron ya samu halartar tsohon shugaban APC na jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye, da Sarki yankin da wasu manyan baki.

Source: Facebook
Da yake mayar da martani, Dr. Nwoye ya yaba wa Sanata Chukwu bisa wannan mataki, yana mai cewa sauya shekar da ya yi zuwa APC abu mai lyau da zai amfanar da shi kansa da kuma al’ummar da yake wakilta.
Jita-jita na neman raba kan 'yan APC
A wani rahoton, kun ji cewa an fara nuna yatsa tsakanin jiga-jigan APC a jihar Enugu kan jita-jitar Gwamna Peter na son shiga jam'iyyar.
Wasu jiga-jigan APC sun fara nuna bacin rai kan yunkurin wasu jagorori na hana Gwamna Peter Mbah shiga jam'iyyar, lamarin da suka ce ba za su lamurta ba.
Sun zargi Ministan Kimiyya da Fasaha, Cif Uche Nnaji, da kokarin toshe duk wata kofa domin kawo cikas ga shirin Gwamna Mbah na shiga APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


