Wike Ya Yaba da Gwamnan PDP Ya Yanke Shawarar Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da sabon titin Ikot Esu–Otomo–Azumini mai tsawon kilomita 15.13 a Akwa Ibom
- Wike ya yabawa Gwamna Umo Eno bisa matakin da ya dauka na hada kai da Shugaban Majalisar Dattawa domin ci gaban jihar
- Gwamna Eno, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, ya jaddada goyon bayansa ga tazarcen Bola Ahmed Tinubu a 2027
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yabawa Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno, bisa kwarin gwiwar barin jam’iyyar PDP tare da komawa APC.
Wike ya yi wannan yabo ne a ranar Laraba yayin kaddamar da titin Ikot Esu–Otomo–Azumini mai tsawon kilomita 15.13 a ƙaramar hukumar Ika ta Jihar Akwa Ibom.

Source: Facebook
Jigon na PDP ya jaddada muhimmancin fifita ci gaba fiye da biyayya ga wata jam’iyya ta siyasa, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya yaba da Gwamna Eno ya bar PDP
Ministan Harkokin Abuja ya ce shawarar da Gwamna Eno ya yanke na yin aiki tare da Shugaban Majalisar Dattawa za ta kawo ƙarin ayyukan ci gaba ga jihar.
“Haɗin kai yana kawo cigaba, yin aiki tare yana kawo cigaba. Dunkule wa wuri daya da ƙarfafa juna yana kawo ci gaba,” in ji shi.
Wike ya yaba wa Eno bisa matakin da ya ɗauka na haɗa hannu da shugaban majalisar dattawa, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa zai samar da karin ayyukan ci gaba a Akwa Ibom.
Wike ya jaddada muhimmancin hadin kai
“Abu mafi kyau da za a yaba wa gwamna shi ne, ya fifita bukatar jihar Akwa Ibom. Domin daga kimar jihar zuwa mataki na gaba, akwai bukatar ya yi aiki tare da shugaban majalisar dattawa.
"Ina tabbatar maku da cewa idan kuka haɗa kai kuka yi aiki tare, za ku ga ƙarin ci gaba a Akwa Ibom.”
- Nyesom Wike.
Ya kuma yaba da irin shugabancin Gwamna Eno, inda ya ce gina titin Ikot Esu–Azumini shaida ce ta jajircewarsa wajen yin ayyukan raya kasa.
Mista Wike ya kawo misali da shugabancin Shugaba Bola Tinubu, inda ya ce gwamnatin Tinubu ta samar da isassun kuɗi ga jihohi don aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

Source: Facebook
Gwamnan ya yi magana kan tazarcen Tinubu
A nasa jawabin, Gwamna Eno ya jaddada muhimmancin haɗin kai wajen kawo ayyukan raya kasa, inda ya ce:
“Idan muka haɗu wajen neman ci gaba, ba siyasa ake kallo ba.”
Gwamna Eno ya gode wa Gwamnan Jihar Abia bisa haɗin kan da ya bashi a aikin titin da ya haɗa jihohin biyu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Eno ya kuma bayyana goyon bayan jihar ga tazarcen Shugaba Tinubu, yana mai cewa shugabancinsa ya fara daidaita tattalin arzikin ƙasa.
Nyesom Wike ya dura kan masu sukarsa
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai bari batanci ko sukar jama’a su yi tasiri a kansa ba.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya fi damuwa da yadda zai bautawa Allah da kuma aiwatar da ayyukan da Bola Tinubu ya dora a wuyansa.
Wike ya kuma nuna damuwa kan yadda jama'a ke sukarsa, yana mai cewa hakan ma kokarin tilasta masa yin abubuwan da bai yi niyya ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


