Shirin Kwace Anambra: APC Ta Kaddamar da Kwamitin Yakin Zabe na Mutane 1,800

Shirin Kwace Anambra: APC Ta Kaddamar da Kwamitin Yakin Zabe na Mutane 1,800

  • APC ta kaddamar da kwamitin kamfen mutum 1,800 a Awka domin doke Gwamna Charles Soludo a Anambra a ranar 8 ga Nuwamba, 2025
  • Nicholas Ukachukwu ya yi alkawarin samar da muhalli mai tsaro, kafa matatar iskar gas da bunkasa harkokin noma idan ya zama gwamna
  • INEC ta fitar da jerin masu kada kuri’a 2,802,790 a Anambra, inda Idemili North ke kan gaba da 246,318 yayin da Anambra West ke can ƙasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - APC ta kaddamar da kwamitin yakin neman zabe mai mutum 1,800 a Awka, domin zaben gwamnan Anambra da za a yi ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Nentawe Yilwatda, ne ya kaddamar da kwamitin bisa wakilcin shugaban APC a Kudu maso Gabas, Ijeoma Arodiogbu.

Jam'iyyar APC ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Anambra
Mambobin jam'iyyar APC yayin da ake kaddamar da yakin neman zaben gwamna a Anambra. Hoto: @SEReporters
Source: Twitter

'Za mu kwace Anambra daga APGA' - APC

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027

Jaridar The Cable ta rahoto Nentawe Yilwatda ya ce jam’iyyar APC na da duk abin da ake bukata domin doke gwamna mai ci, Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yilwatda ya ce jam’iyyar APC zata yi amfani da dukkan albarkatunta wajen kwace mulki daga hannun APGA a dokance.

Shugaban jam'iyyar ya ce:

“Anambra tana da matukar muhimmanci ga shugabancin APC na kasa. Mun zaɓe ku ne saboda mun yi imani cewa za ku iya yin wannan aikin.”

Ya kara da cewa dukkanin shugabannin APC na Kudu maso Gabas, gwamnan Imo, Hope Uzodimma, shugabancin kasa da Shugaba Bola Tinubu, na tare da su.

Anambra: 'Dan takarar APC ya dauki alkawura

'Dan takarar gwamna na APC, Nicholas Ukachukwu, ya yi kira ga mambobin jam’iyya da jama’ar Anambra su mara masa baya a zaben jihar mai zuwa..

Ya sha alwashin samar da yanayi mai kyau na kasuwanci, ilimi, da sauran bangarori da z su bunkasa tattalin arzikin jihar idan aka zabesa.

Ukachukwu ya kuma yi alkawarin kafa matatar iskar gas domin samar da wutar lantarki da cigaban masana’antu.

Kara karanta wannan

APC, ADC da PDP sun 'ayyana' wanda suke fata Tinubu ya ba shugaban INEC

Bugu da ƙari, ya ce zai inganta sashen noma tare da inshorar manoma domin bunkasa noma na zamani.

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa mutane 2,802,790 ne za su kada kuri'a zaben gwamnan jihar Anambra.
Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, zaune a wajen wani taro a Abuja. Hoto: @inecnigeria
Source: Getty Images

Anambra: INEC ta fitar da bayanan masu zabe

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa mutane 2,802,790 ne za su kada kuri'a zaben gwamnan jihar Anambra da za a yi a Nuwamba, kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.

A cikin sanarwar da shugaban kwamitin yada labarai na INEC, Sam Olumekun, ya fitar ranar 4 ga Satumba, INEC ta ce an samu karin ne bayan tantance sababbin masu rajista.

A cikin jerin, karamar hukumar Idemili ce ta fi yawan masu kada kuri'a da mutane 246,318 (8.79%), sai Awka ta Kudu da mutane 216,611 (7.73%), sannan Ogbaru da 188,016 (6.71%).

Rahoton ya nuna cewa karamar hukumar Dunukofia na da masu kada kuri'a 83,580 (2.98%), yayin da Anambra ta Yamma ke da mafi ƙanƙantar masu zabe, 71,332 (2.55%).

Anambra: Abin da zai hana APGA samun tazarce

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gangar siyasa ta kada yayin da wa’adin farko na Chukwuma Charles Soludo a matsayin gwamnan Anambra ya zo karshe.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Shugaban APC ya rikita 'yan adawa kan zaben 2027

A Nuwambar 2025, al’ummar Anambra za su koma rumfunan zabe domin sake zaben Gwamna Soludo ko kuma su goyi bayan wani sabon shugaba.

Tun daga rikicin harkokin addini da Gwamna Soludo ya jefa kansa, har zuwa ga barazanar jam'iyyun adawa, ana ganin dalilai biyar za su iya hana shi samun tazarce.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com