Yadda Tinubu da Atiku ke Kokuwar Kwace Magoya bayan Buhari na Arewa

Yadda Tinubu da Atiku ke Kokuwar Kwace Magoya bayan Buhari na Arewa

  • Wasu manyan magoya bayan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari sun bayyana goyon baya ga Atiku Abubakar a Abuja
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara Kaduna inda ya gana da iyalan Buhari yayin auren dan Sanata Abdulaziz Yari
  • Masana na hasashen hakan wata manuniya ce kan yadda shugaban kasar da babban abokin hamayyarsa ke neman nasara a 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Siyasar Najeriya na kara daukar zafi yayin da ake shirye-shiryen zaben 2027, inda neman shawo kan magoya bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito fili.

Kokuwar janyo magoya bayan Buhari na faruwa ne tsakanin shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Atiku, Buhari da shugaban kasa Bola Tinubu.
Atiku, Buhari da shugaban kasa Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Bashir Ahmad
Source: Facebook

Vanguard ta hada wani rahoto na musamman kan alamomin da ke nuna cewa 'yan siyasar na neman shawo kan magoya bayan Buhari.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya shawarci Atiku Peter Obi kan takara da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan CPC sun koma wajen Atiku Abubakar

Kwanan nan, wasu shugabannin jihohi na tsohuwar CPC sun gana da Atiku Abubakar a Abuja inda suka ayyana goyon bayansu gare shi.

Sun bayyana cewa su ne sahihan magoya bayan Buhari kuma suna ganin wajibi a fito fili wajen karfafa siyasa maimakon yinta a boye.

Punch ta wallafa cewa wani daga cikinsu ya jaddada cewa:

“Buhari ya bar tarihi mai girma a Najeriya, kuma ba za mu bari wannan tarihi ya lalace ba.”
Yadda wasu 'yan APC da mutanen Atiku suka ziyarci Buhari kafin ya rasu
Yadda wasu 'yan APC da mutanen Atiku suka ziyarci Buhari kafin ya rasu. Hoto: Atiku Abubakar|All Progressive Congress
Source: Twitter

Atiku ya rungumi magoya bayan Buhari

Da yake mayar da martani, Atiku ya nuna farin cikinsa da tarbar tsofaffin shugabannin CPC, yana mai cewa wannan hadin kai wani bangare ne na ci gaba da gwagwarmayar siyasa da ya fara.

Ya yi kira gare su da su shiga cikin rajistar masu kada kuri’a, yana mai jan hankali cewa goyon baya da alaka ba za su wadatar ba idan ba a nemi kuri’un zabe ba.

Kara karanta wannan

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mahmood Yakubu a shugabancin INEC

Tinubu ya ziyarci iyalan Buhari a Kaduna

A daidai lokacin da wasu 'yan CPC suka nuna goyon baya ga Atiku, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Kaduna.

Ya halarci bikin ɗan Sanata Abdul’aziz Yari sannan ya je gidan marigayi Buhari inda ya gana da Hajiya Aisha Buhari.

Duk da cewa an ce ziyara ce ta girmamawa, masu fashin baki sun ce tana ɗauke da babban sako na siyasa; Tinubu na son tabbatar da cewa shi ne magajin siyasar Buhari a idon jama’a.

Ana kokarin kwace mutanen Buhari

Wasu daga cikin magoya bayan CPC suna ganin APC ta kauce daga akidun da suka kafa ta, suna danganta hakan da jagorancin Tinubu a lokacin da suka karkata wajen Atiku.

A gefe guda kuma, Tinubu na kokarin amfani da ziyara da hulɗa da iyalan Buhari domin tabbatar da kansa a matsayin magajin Buhari da ya ke gini kan tubalin da marigayin ya kafa.

Tinubu zai bar mulkin Najeriya a 2031

Kara karanta wannan

Atiku ko Tinubu: Kawunan magoya bayan Buhari na CPC ya rabu a kan zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i martani kan cewa Tinubu zai nemi zama a mulki har abada.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa Bola Tinubu zai sauka daga mulki idan ya kammala wa'adi na biyu bayan tazarce.

Hakan na zuwa ne bayan Nasir El-Rufa'i ya yi ikirarin cewa shugaban kasar zai zama kamar Paul Biya na Kamaru idan ya zarce a 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng