Atiku ko Peter Obi: Kungiya Ta Fadi wanda Ya Kamata Ya Hakura da Takara a 2027
- Ana ci gaba da tattaunawar siyasa kan batun zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara
- Wata kungiya mai suna SDMA ta fito ta yi kira wanda ya shafi Atiku Abubakar da Peter Obi dangane da zaben
- Kungiyar ta nuna hadarin da ke tattare da yin takararsu a karkashin inuwar jam'iyyu daban-daban
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kungiyar Save Democracy Mega Alliance (SDMA) ta yi kira da babbar murya ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Kungiyar ta bukaci Atiku ya karɓi matsayin jagora ɗan kishin kasa, kuma dattijo mai hangen nesa, ta hanyar marawa Peter Obi baya ya zama ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban ta, Prince Tony Akeni, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan
Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An jira ra'ayin jama'a kan zaben 2027
Kungigar ta ce an ji ra'ayin jama'a bayan mulkin shekaru takwas na marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.
Ta ce binciken ra’ayin jama’a ya nuna cewa sama da kaso 90 cikin 100 na ’yan Najeriya daga mafi yawan jihohin Kudu da kuma jihohin Arewa ta Tsakiya sun yanke shawarar mara wa ɗan takarar Kudu baya.
Ƙungiyar ta kara da cewa maimakon sake zaɓen wani ɗan Arewa a 2027, wanda hakan zai ci gaba da tauye ’yan Kudu daga samun wa’adin mulki na tsawon shekaru takwas, sun sha alwashin cewa za su mara wa Tinubu baya don yin wa’adi na biyu.
Sai dai kuma, ta ce zaɓen 2027 wata dama ce ga ’yan Najeriya kusan miliyan 230 don kawo ƙarshen mulkin jam'iyyar APC, rahoton The Guardian ya tabbatar da labarin.
Kungiya ta ja kunnen 'yan adawa
Ƙungiyar ta kuma yi gargadin cewa idan shugabannin adawa suka yi rashin nasara a zaben 2027, saboda daukar matakan da ba su dace ba, hakan kan zai iya haifar wa kasar nan mummunan sakamako iri-iri.
"Najeriya tana da manyan ’yan adawa guda biyu, kowannensu ya cancanci ya shugabanci kasarmu a matsayin shugaban kasa daga shekarar 2027 don dawo da kasar nan kan tafarkin da ya dace."
"Waɗannan mutanen sune Atiku Abubakar na jam’iyyar ADC, da Peter Obi, wanda yake a LP."
- Prince Tony Akeni

Source: Facebook
SDMA ta yi zargin cewa APC ta dana wasu turaku don hana gudanar da sahihin zaɓe, wadanda za su hana Atiku ko Peter Obi damar samun nasara idan suka tsaya takara daban-daban.
"Muna rokon ka yi hakan saboda kasarmu, ta hanyar sanya albarkarka, goyon baya ga Peter Obi don ya zama dan takarar shugaban kasa na adawa a madadin ’yan Najeriya gaba ɗaya domin tunkarar APC a 2027."
- Prince Tony Akeni
Atiku ya ziyarci Sheikh Pantami
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyara ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon ministan sadarwan ne a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja.
A yayin ziyarar, manyan mutanen guda biyu sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
