Sauya Sheka: An Fadawa Tinubu Yadda Kwankwaso zai Taimaka Masa a 2027

Sauya Sheka: An Fadawa Tinubu Yadda Kwankwaso zai Taimaka Masa a 2027

  • Babban jigon APC, Sam Nkire, ya ce dawowar Rabiu Musa Kwankwaso jam’iyyar zai tabbatar da nasarar Bola Tinubu
  • Ya yi kira ga shugaban ƙasa Tinubu da ya yi duk mai yiwuwa domin dawo da tsohon gwamnan Kano cikin jam’iyyar
  • Nkire ya ce tsohuwar alaƙar siyasa da abokanta tsakanin Tinubu da Kwankwaso za ta iya sauƙaƙa yarjejeniyar komawarsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Babban jigon jam’iyyar APC, Sam Nkire, ya yi magana kan zancen komawar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso jam'iyya mai mulki.

Ya bayyana cewa idan Rabiu Musa Kwankwaso ya koma cikin APC, hakan zai tabbatar da nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓe na 2027.

Sanata Rabiu Kwankwaso tare da shugaba Tinubu
Sanata Rabiu Kwankwaso tare da shugaba Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

The Guardian ta wallafa cewa ya ce haɗa kai da Kwankwaso zai ƙarfafa tabbacin nasarar Bola Tinubu da kuma shawo kan sauran jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

'Ba da mu ba,' NNPP ta nesanta kanta da shirin Kwankwaso na shiga APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nkire ya yi wannan jawabi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya yi kira ga Tinubu da ya yi duk mai yiwuwa domin jawo Kwankwaso zuwa jam’iyya mai mulki.

Kiran dawo da Rabiu Kwankwaso cikin APC

Nkire ya bayyana cewa dawowar Kwankwaso APC ba wai kawai za ta ƙara ƙarfin jam’iyyar ba ne, har ma za ta tabbatar da goyon bayan da ake buƙata musamman a Arewa.

Ya yi kira da cewa ya kamata Tinubu ya yi amfani da kwarewarsa a harkokin siyasa da kasuwanci wajen cimma yarjejeniya da tsohon abokin siyasarsa.

“Ko da Tinubu zai yi nasara, shigar Kwankwaso APC za ta rufe kofar shakku,”

- In ji shi.

Dangantakar Shugaba Tinubu da Kwankwaso

Nkire ya tuna yadda ya kasance tare da Kwankwaso a 2014 lokacin da suka kai ziyara wurin Bola Tinubu.

Ya ce a lokacin Tinubu jagora ne a APC kuma sun je wajen sa ne neman goyon baya ga Kwankwaso a fafatawar neman takarar shugaban ƙasa da Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Da gaske Tinubu zai zauna a mulki har ya mutu? Fadar shugaban kasa ta magantu

Sai dai a lokacin, Tinubu ya bayyana cewa ya riga ya yi alƙawari ga marigayi Muhammadu Buhari.

Nkire ya ce wannan tarihi na nuna cewa babu wata baraka ta kashin kai tsakanin Tinubu da Kwankwaso, kuma hakan na nufin akwai damar sake haɗuwa a siyasa.

Nkire ya yarda a kulla yarjejeniya

Nkire ya ce ya aminta da kulla yarjejeniya da Tinubu, wanda ya jaddada cewa ya saba da mu’amala da manyan yarjejeniyoyi ba tare da saba su ba.

Ya ƙara da cewa dawowar Kwankwaso za ta ba da damar samar da cikakken haɗin kai tsakanin shugabancin ƙasa da wasu manyan jiga-jigan Arewa.

A cewar Nkire, hakan zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban dimokuraɗiyya a Najeriya.

Sanata Rabiu Kwankwaso yana hira da 'yan jarida
Sanata Rabiu Kwankwaso yana hira da 'yan jarida. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jam'iyyar NNPP ta barranta da Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa tsagin jam'iyyar APC ya yi Allah wadai da maganar shiga APC da Kwankwaso ya yi a baya.

Tsagin jam'iyyar ya bayyana cewa ya dade da koran Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya saboda matsalolinsu.

Kara karanta wannan

El Rufai ya gargadi 'yan Najeriya kan Tinubu, ya yi hasashen shirinsa kan mulki

Ya kara da cewa yanzu haka NNPP ta fara shirye shiryen tunkarar zaben shugaban kasa da na jihohi bayan sallamar Kwankwaso da mutanensa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng