Jita Jitar Gwamna na Shirin Ficewa daga PDP zuwa APC Ta Fara Tayar da Kura

Jita Jitar Gwamna na Shirin Ficewa daga PDP zuwa APC Ta Fara Tayar da Kura

  • Wasu jiga-jigan APC reshen jihar Enugu sun fara nuna bacin rai kan yunkurin wasu jagorori na hana Gwamna Peter Mbah shiga jam'iyyar
  • Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu na cikin gwamnonin PDP da ake rade-radin za su iya sauya sheka zuwa APC kafin 2027
  • Ana zargin Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire, Uche Nnaji na cikin wadanda ke kokarin hana Gwamna Mbah shiga APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Jiga-jigan APC a Jihar Enugu sun nuna damuwa kan yunkurin wasu daga cikin shugabannin jam'iyya na hana Gwamna Peter Mbah sauya sheka.

A cewar 'yan siyasar, sun fara ganin alamun wasu shugabannin jam'iyyar na neman kashe gwiwar Gwamnan Enugu, Peter Mbah ya fasa sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu.
Hoton Gwamna Peter Mbah a fadar gwamnatin jihar Enugu Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Source: Twitter

'Yan APC sun yi barazanar fita zanga-zanga

Kara karanta wannan

'Yan APC sun ankarar da Shugaba Tinubu kan gwamnonin da zai yi hattara da su

Sun yi barazanar gudanar da zanga-zanga a Abuja idan har aka ci gaba da ƙoƙarin hana Gwamna Peter Mbah komawa jam’iyyar APC, in ji rahoton Vanguard.

Wannan gargaɗin ya fito ne a ƙarshen mako bayan taron jiga-jigan jam’iyyar APC daga ƙananan hukumomi shida na mazabar Enugu ta Gabas.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon shugaban APC na Enugu, Dr. Ben Nwoye; tsohon jakadan Najeriya a Ukraine, Janar Christian Ugwu; da tsohon Shugaban Jami’ar Michael Okpara da ke Umudike, Farfesa Hilary Edoga.

Sauran sun hada da tsohon ɗan takarar gwamna, Cif Gab Nnamani; Cif Anike Nwoga; Hon. Hyacinth Ngwu; da Hajiya Juliet Egbo, rahoton The Nation.

Kan yan APC ya fara rabuwa a Enugu

Sun zargi Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Cif Uche Nnaji, da kokarin toshe duk wata kofa domin kawo cikas ga shirin Gwamna Mbah na shiga APC,

Dr. Nwoye ya bayyana cewa sauya shekar Gwamna Mbah zuwa APC zai sauya rashin sa'ar jam’iyyar a Jihar Enugu, yana mai jaddada cewa gwamnan ya karbu a wurin jama’a.

"Burinmu shi ne mu sauya tarihin rashin sa'ar APC a Enugu, ana ta yada jita-jitar cewa Gwamna Mbah zai dawo APC saboda yadda yake kokari.

Kara karanta wannan

El Rufai ya gargadi 'yan Najeriya kan Tinubu, ya yi hasashen shirinsa kan mulki

"Amma wasu na kokarin hana hakan, ba su son gwamna ya dawo APC saboda son zuciya, ba za mu bar hakan ta faru ba," in ji shi.

Rahoton sauya shekar gwamna ya tada kura

Ya ƙara da cewa kokarin da Mbah ke yi a fannin hanyoyi, ilimi, kiwon lafiya da tsaro sun samu yabo daga Shugaba Bola Tinubu duk da bambancin siyasa da ke tsakaninsu.

Tutar APC.
Hoton tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: OfficiaAPCNig
Source: Getty Images

A nasa bangaren, Cif Anike Nwoga ya gargadi cewa idan ministan da abokan aikinsa suka ci gaba da kokarin hana gwamna Mbah shiga APC, za su yi tattaki zuwa fadar shugaban ƙasa domin neman tsige shi.

“APC ba ta taɓa lashe manyan kujeru a Enugu ba. Idan Peter Mbah ya shigo, alama ce ta jam’iyyar za ta fara yin nasara. Wasu suna son APC ta sha kashi a 2027 domin su ci gaba da riƙe mukaman Abuja,” in ji shi.

Ministan Tinubu ya yabi Gwamna Mbah

A wani rahoton, kun ji cewa Festus Keyamo ya fito ya nuna cewa Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana tsoron karawa da Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Shugaban APC ya rikita 'yan adawa kan zaben 2027

Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Saman ya ce suna tsoron gwamnan ne saboda ayyukan da yake yi wadanda za su taimakawa rayuwar al'umma.

Keyamo ya ce Gwamna Mbah yana daya daga cikin gwamnonin da suka fi kowa kyakkyawan aiki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262