2027: Yadda Kwankwaso Ya Sha Yabo da Raddi kan Maganar Yiwuwar Shiga APC

2027: Yadda Kwankwaso Ya Sha Yabo da Raddi kan Maganar Yiwuwar Shiga APC

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce su ne suka fara kafa jam’iyyar APC duk da matsalolin da suka fuskanta
  • Kwankwaso ya yi nuni da cewa su da suke NNPP za su iya komawa APC idan aka ba su tabbacin makoma mai kyau
  • Maganar tasa ta jawo martani daga magoya bayan ADC, tsofaffin jami’an gwamnati da kuma ‘yan jam’iyyar APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake bayyana alakar sa da jam’iyyar APC tare da yiwuwar sake shiga cikinta, amma da sharadi.

Kwankwaso ya ce su ne suka jagoranci kafa jam’iyyar a wancan lokaci, duk da tsananin matsin lamba daga hukumomin gwamnati da jami’an tsaro.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana wani jawabi a Kano
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana wani jawabi a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad na cikin 'yan jam'iyyar APC da suka yi martani kan kalaman Kwankwaso a Facebook.

Kara karanta wannan

A wani matsayi za a karbi NNPP, Kwankwaso ya yi maganar yiwuwar shiga APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharadin da Rabiu Kwankwaso ya gindaya

Sanata Kwankwaso ya nuna cewa a shirye jam’iyyar NNPP take ta sauya sheka zuwa APC, amma sai an tabbatar musu da abin da za su samu.

A cewarsa, babu jihar da ba su da ‘yan takarar gwamnoni, Sanatoci da shugabannin jihohi a NNPP, don haka dole APC ta tabbatar musu da makoma kafin su dawo.

Martanin jama'a kan kalaman Kwankwaso

Dr Usman Isyaku da ke goyon bayan Atiku Abubakar, ya wallafa a Facebook cewa:

“Sun ce Atiku bai damu da talaka ba, Kwankwaso kuma jagoran talakawa. To ta yaya hakan zai yiwu idan yanzu yana neman haɗin kai da Tinubu?

Hadimin marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya yabawa Kwankwaso da cewa:

“Duk lokacin da Madugu ya shirya, muna yi masa maraba.”
"Har yanzu Kwankwaso yana son shiga APC, jam'iyyar ma na so ya shiga. Me ake jira ne kenan?

Kara karanta wannan

NECO: Kwankwaso ya yabi aikin Abba bayan daliban Kano sun doke na sauran jihohi

Dan APC mai biyayya ga marigayi Buhari, Cham Faliya Sharon tsokanar 'yan Kwankwasiyya ya yi a Facebook da cewa:

“Idan aka ba Kwankwaso buhun rogo guda da matsayin jagoran APC na Nyanya, zai bar NNPP ya dawo APC.”
Kwankwaso tare da Abba Kabir Yusuf
Kwankwaso tare da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

Haka kuma, tsohon kwamishina a gwamnatin Abdullahi Ganduje a Kano, Muaz Magaji, ya wallafa a Facebook cewa kawai:

“An dawo wajen!”

Imrana Daura ya wallafa a Facebook cewa:

“Kwankwaso ya yi maganar komawa APC amma babu wani tsari mai tabbas da aka yi masa. Ba wanda ya yi masa alkawari kan abin da zai samu shi da magoya bayansa.
"Wannan ya nuna cewa sha’anin siyasar Kwankwaso na kansa ne, ba na al’ummar Arewa baki daya ba.”

Kwankwaso ya yaba wa Abba Kabir

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana bayan jihar Kano ta zamo ta daya a jarrabawar NECO ta 2025.

Sanata Kwankwaso ya jinjina wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf bisa nasarar da jihar ta samu a jarrabawar.

Kara karanta wannan

Yayin da Kwankwaso ke taro a Kano, Barau ya janye 'yan NNPP zuwa APC

Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso ya taya daliban jihar Kano murna bisa rawar gani da suka taka a fadin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng