ADC Ta Fadi Gwamnan da Doka Ta Yarje wa Tinubu Ya Sauke daga Kujerarsa
- Jam'iyyar hamayya ta ADC ta bayyana matsayarta a kan dakatar wa da dawo da zababben jihar Ribas, Siminalayi Fubara
- ADC, ta bakin kakakinta, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa wannan al'amari daidai ya ke da mulkin kama karya a kasar nan
- Ya bayyana cewa wannan al'amari abin damu wa ne, musamman ganin yadda ake zargin Tinubu ya maida batun kamar kishin kasa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Jam'iyyar ADC ta bayyana takaicin yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ketare doka wajen dakatar da zababben Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara.
Mai Magana da Yawun Jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ne kadai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke da ikon ya sauke ko ya nada.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Bolaji Abdullahi a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025, ya caccaki shugaban kasar bisa matakin da ya dauka na dakatar wa da dawo da Fubara a ganin damarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar ADC ta caccaki Bola Tinubu
Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa cin mutuncin dimokuradiyya ne matakin da Bola Tinubu ya dauka da ikon gwamnatin tarayya.
A cewar Bolaji Abdullahi:
“Gwamna daya tilo da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke da ikon dakatarwa ko naɗa shi shi ne Yemi Cardoso. Ba shi da wannan ikon a kan gwamnan jiha.”

Source: Facebook
Ya kara da cewa:
“Yadda shugaban kasa Tinubu ya dakatar da zababben Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sannan ya dawo da shi ba tare da wani tsari ba, alamar mulkin kama-karya ne."
“Ya kamata Shugaban kasa Tinubu ya kanannade abin da ke ra'ayin siyasa dda sunan kishin kasa ba.
“Dakatar da Gwamnan Ribas abu ne da ya amfanar da kansa \(Tinubu) kawai, kuma ba bisa kundin tsarin mulki ba ne.”
Yadda Tinubu ya dakatar da Gwamnan Ribas
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara da wasu ‘yan majalisar dokoki na jihar Ribas tun a watan Maris.
Ya dauki matakin ne a dalilin rikicin siyasa da ya kunno kai tsakanin Fubara da tsohon gwamna kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Tinubu ya bayyana dokar ta baci a jihar Ribas a lokacin, yana mai cewa akwai barazanar rikici da ka iya lalata zaman lafiya da tsaron jama'a.
Sai dai, Bolaji Abdullahi na jam’iyyar ADC ya soki wannan mataki, yana mai cewa shugaban kasa ba shi da hurumin daukar irin wannan mataki kan gwamnan jiha.
ADC ta yi martani ga jigon LP
A baya, mun wallafa cewa Jam’iyyar ADC ta maida martani mai zafi kan kalaman da Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi a kan 'yan adawa da su ka shiga hadaka kalubalantar APC.
'Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, ya yi, inda ya zargi hadakar 'yan adawa da yaudarar 'yan adawa da su ke son kwace mulki a hannun Tinubu.
Jam’iyyar ADC ta jaddada cewa manufar hadakar ita ce kawo karshen gwamnatin APC a zaben 2027, ta hanyar hada manyan 'yan siyasa domin samar Shugabanci na gari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


