PDP Ta Fara Rokon Fubara bayan APC Ta Yi Masa Tayin Sauya Sheka
- PDP ta roƙi Gwamna Fubara da kada ya bar jam’iyyar, bayan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya maido shi bakin aiki
- Watanni shida baya ne Shugaban ya dakatar da Gwamna Fubara, Mataimakiyarsa da 'Yan Majalisar jihar saboda rikicin siyasa
- A yau Alhamis, 18 ga watan Satumba ne Fubara da sauran mutanen da Shugaban kasa ya dakatar su ka koma bakin aiki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers– Jam’iyyar PDP reshen Jihar Legas ta roƙi Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers da kada ya fice daga jam’iyyar, bayan da aka dawo da shi ofis.
A ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025 ne Gwamna Fubara, Mataimakiyarsa da 'yan majalisar jihar su ka koma bakin aiki bayan Shugaba Bola Tinubu ya janye dokar ta baci a jihar.

Source: Instagram
PM News ta wallafa cewa ana zargin Tinubu ya sanya dokar ta bacin ne saboda rikicin siyasa a tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta taushi Gwamnan Ribas, Fubara
Mataimakin Shugaban PDP na Legas ta Tsakiya, Hakeem Olalemi, ya shawarci Fubara da kada ya bari tsoron siyasa ya hana shi aiwatar da nagartaccen shugabanci.
Ya ce:
“Kada Gwamna ya nuna tsoro, abin da ya faru ya faru. Ya ci gaba da jajircewa da yi wa jihar hidima yadda ya kamata.”
Olalemi ya kuma roƙi Fubara da kada ya yi watsi da jam’iyyar PDP wadda ta ba shi damar zuwa kujerar mulkin jama'ar Ribas.
Ya ce:
“Ya kula da jam’iyyar da ta kawo shi kan mulki, kada ya barta. Ya tabbatar da cewa PDP ta ƙara ƙarfi a Ribas.”
Jam'iyyar PDP ta shawarci 'yan siyasa
Mataimakin Shugaban PDP na Legas ta Tsakiya, Hakeem Olalemi, ya dukkanin 'yan siyasa a jihar Ribas da su zubar da makamansu, su kuma rungumi zaman lafiya.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

Source: Twitter
Ya bayyana cewa:
“Bai kamata mu rika murna ko shagulgula cewa Fubara ya dawo ofis ba. Wannan dama ce da al’umma suka ba shi, amma yanzu an rage ƙarfinta. ‘Yan majalisa da na zartarwa su haɗa kai su yi aiki don al’umma, su daina siyasa kawai.”
Olalemi ya ƙara da cewa, ‘yan majalisa 27 da suka bi jam’iyyar APC sakamakon rikicin, su dawo PDP su taimaka wajen gina jam’iyyar da jihar.
Ribas: Wike ya mika sako ga Tinubu
A baya kun ji cewa Ministan babban Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana godiyarsa da yabawa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakin da ya dauka na janye dokar ta-baci a Ribas.
Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun bakin ministan, Lere Olayinka, a daidai lokacin da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya koma bakin aikinsa.
A cewar Nyesom Wike, Tinubu ya sake nuna cewa yana da gaskiya da jajircewa wajen kare tsarin zaman lafiya da cigaban dimokuraɗiyya a fadin Najeriya baki ɗaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

