Kalaman Ministan Buhari Sun Jefa Shi a Matsala, Za a Shiga Kotu kan Zarin Gwamna

Kalaman Ministan Buhari Sun Jefa Shi a Matsala, Za a Shiga Kotu kan Zarin Gwamna

  • Gwamnatin jihar ta yanke shawarar kai tsohon minista a mulkin Muhammadu Buhari, Abubakar Malami kotu
  • Wannan na zuwa ne bayan zarginsa da bata suna wanda ya ke zargin gwamnatin jihar da daukar nauyin ta'addanci
  • Hadimin gwamnan Kebbi ya zargi Malami da yada kalaman karya kan gwamnati ya ce bai taimaka wa jama’a ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin jihar Kebbi da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami.

Ana zargin Malami da fadan wasu kalamai da kuma zargin gwamnatin jihar da daukar nauyin ta'addanci wanda ya jawo magana a jihar.

Malami zai iya fuskantar matsala kan zargin gwamna
Gwamna Nasir Idris na Kebbi da tsohon minista, Abubakar Malamai. Hoto: Abubakar Malamai SAN.
Source: Facebook

Kebbi: Shirin da al'umma ke yi kan Malami

Hadimin gwamnan Kebbi a bangaren ayyuka na musamman, Shafi’u Abubakar Shattiman Zauro shi ya tabbatar da haka a sanarwar da AIT News ta samu.

Kara karanta wannan

Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi

Shafi'u ya ce mutanen jihar Kebbi sun bayyana shirin daukar matakin doka kan tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN.

Majiyoyi sun ce ana zargin tsohon ministan a mulkin marigayi Muhammadu Buhari bisa zargin bata suna da rura rikici.

Abin da ake zargin Malami da furtawa

Ya ce Malami ya yi wasu kalaman karya yana zargin gwamnatin jihar Kebbi da daukar nauyin ta’addanci, abin da ya haifar da ce-ce-ku-ce sosai.

Shattiman ya ce:

“Yawancinmu da muka san Malami ba mu yi mamakin hakan ba. Ya taba kai Atiku kotu kan ƙasar haihuwa.”

Ya kuma kara da cewa Malami ya taba kai Wambam Koko, wanda yanzu abokin tafiyarsa ne, EFCC da ICPC saboda son takarar gwamna.

An taso tsohon minista kan zargin gwamnan Kebbi
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi a ofis. Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu.
Source: Facebook

An kalubalanci Malami kan ayyukan alheri

Shafi'u ya ce Malami bai taba taimakawa ci gaban jihar Kebbi ba, ko ma makarantar firamare Junju da ya yi karatu a ciki.

Ya ce jihar Kebbi ta shahara da zaman lafiya, amma Malami ba ya jin daɗin nasarorin da Gwamna Nasir Idris ya samu wajen ci gaban jihar.

Kara karanta wannan

Sulhu ya kankama, gwamna ya kawo shirin da za a tallafawa tubabbun 'yan bindiga

A cewarsa, gwamnan ya jawo zuba hannun jari musamman a bangaren ma’adinai, wanda hakan ya haddasa kishin Malami saboda bai iya yi a lokacin sa ba.

An yabawa Gwamna Idris na jihar Kebbi

Shafi'u ya kara da cewa a lokacin da gwamna Idris ke maida hankali kan cigaba, Malami shi ne ke haddasa rikici da rudani kawai, cewar Channels TV.

Ya kammala da cewa:

“Don haka al’ummar jihar Kebbi sun yanke shawarar daukar matakin doka kan Malami saboda bata suna da tayar da zaune-tsaye.”

'Yan majalisa sun taso Malami a gaba

A wani labarin, rigimar siyasar jihar Kebbi ya kara kamari tun bayan farmakin da ake zargin an kai wa tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami.

Tawagar yan Majalisar Tarayya daga Kebbi sun yi watsi da zarge-zargen da Malami SAN ya yi wa Gwamna Nasir Idris wanda ya tayar da kayar baya a jihar.

Sun bukaci hukumomin tsaro su kama tsohon babban lauyan na gwamnati domin ya yi bayani kan abubuwan da ya fada a korafinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.