Mutanen Buhari na CPC Sun Gana da Atiku, Sun Shiga ADC don Kifar da Tinubu

Mutanen Buhari na CPC Sun Gana da Atiku, Sun Shiga ADC don Kifar da Tinubu

  • Tsofaffin shugabannin jihohi na CPC sun kai ziyara ga Atiku Abubakar a Abuja domin nuna goyon baya ga shirin kayar da APC
  • Atiku Abubakar ya bayyana musu yadda aka fara kafa hadakar ADC a matsayin sabon dandalin siyasa mai karfin jama’a
  • Shugabannin sun zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da kauce wa manufofin da suka tallafa wa talakawa tun asalin kafa APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsofaffin shugabannin jam’iyyar CPC da aka rusa a baya sun kai ziyara wajen tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a gidansa da ke Abuja.

Shugabannin sun bayyana goyon bayansu ga shirin da yake jagoranta na kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

'Yan CPC yayin ganawa da Atiku Abubakar a Abuja
'Yan CPC yayin ganawa da Atiku a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku Abubakar bayyana abubuwan da suka tattauna da shugabannin a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin sun nuna damuwarsu cewa gwamnatin Tinubu ta kauce daga manufofin kula da rayuwar talakawa, wanda a cewarsu shi ne ginshikin da aka kafa APC a kai tun farko.

Atiku ya karɓi shugabannin CPC

Bayan ganawar, Atiku ya bayyana cewa ya yi bayani dalla-dalla kan yadda aka kulla shirin kafa hadakar siyasa da nufin karfafa dandalin da zai maye gurbin APC.

Ya ce, manufar ADC ita ce samar da sabon tsari da zai kawo sauyi, tare da ba da fifiko ga bukatun al’umma.

Ya kuma karfafa gwiwar shugabannin da su tura magoya bayansu zuwa cibiyoyin rajistar masu kada kuri’a, domin tabbatar da shigar jama’a cikin tsarin zabe mai zuwa.

'Yan tsagin CPC sun soki Tinubu

A lokacin ganawar, shugabannin tsohuwar CPC sun bayyana takaicinsu kan yadda gwamnatin APC ta yanzu ta bijire daga manufofin da aka kafa ta a kai.

The Guardian ta rahoto cewa shugabannin sun yi zargin cewa an yi watsi da manufofin tallafawa talakawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi dalilin janye dokar ta baci a Rivers

Atiku da Buhari a Kaduna
Lokacin da El-Rufa'i da Atiku suka ziyarci Buhari a Kaduna. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Sun ce manufofin Tinubu sun gaza karfafa tattalin arzikin kasa ko magance matsalolin da ke addabar jama’a, abin da ya tilasta su nemi sabon dandalin da zai kare muradun al’umma.

Atiku ya yi amfani da ganawar wajen bayyana yadda aka fara kafa dandalin hadaka na ADC, wanda ya ce dandalin jama’a ne da zai yi aiki wajen samar da sauyi a siyasar Najeriya.

'Yan Buhari a CPC sun shiga ADC

Atiku ya nanata cewa shirin kafa dandalin ADC yana kan gaba wajen kawo sabuwar tafiya ga jama’ar Najeriya.

Ya bayyana hadin gwiwar da yake nema a matsayin hanyar kifar da gwamnati mai ci da kuma gina sabon tsarin da zai mayar da adalci da gaskiya cikin harkokin mulki.

Shugabannin CPC sun bayyana cewa za su taka rawa wajen yada ADC a yankunansu, domin tabbatar da cewa an cimma burin da ake nema na kafa sabuwar gwamnati.

Kara karanta wannan

Dogara ya bankado abubuwan da ya ce Buhari ya lalata kafin ba Tinubu mulki

Dogara ya ce Buhari ya rusa tattali

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya kare gwamnatin Bola Tinubu kan halin da kasa ke ciki.

Tsohon dan majalisar ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ce ta fara lalata tattalin kasa kafin zuwan Bola Tinubu.

Baya ga haka, ya kara da cewa a yanzu haka gwamnatin Tinubu tana kan shirye shiryen gyara matsalolin da aka samu a baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng