2027: APC, PDP Sun Fara Nuna wa Juna Yatsa kan Karya Dokar INEC

2027: APC, PDP Sun Fara Nuna wa Juna Yatsa kan Karya Dokar INEC

  • APC da PDP sun fara cacar baki dangane da kamfen dda ta ke zargin APC mai mulki ta fara tun kafin lokacin da aka ware don yin haka
  • Jam'iyyar, reshen jihar Legas ta yi takaicin yadda ake kokarin yi wa Bola Tinubu kamfen da sunan nuna goyon baya ga Shugaban Kasa
  • Sai dai APC ta yi martani, inda ta ce PDP ta rikice, kuma yadda 'ya'yanta ke sauya sheka zuwa cikinta ya nuna cewa lamari ya kacame mata

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaAPC mai mulkin Najeriya da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP sun fara cacar baki a kan zargin fara gangamin neman kuri'ar 'yan kasa da wuri.

Jam'iyyar PDP ta caccaki APC kan zargin yakin neman zabe a yanzu, duk da hakan ya saba da dokar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan Neja, Bago ya fadi abin da zai tilasta wa Arewa zaben Tinubu

PDP ta caccaki APC kan zaben 2027
Hoton Shugaban PDP na kasa, Umar Iliya Damagum/Shugaban Kasa, Bola Tinubu Hoto: Umar Damagum/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, fara kamfen a fakaice da APC ta yi, alamu ne da ke nuna cewa ta tsorata matuka da zabean 2027 mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta fara tattaro wa Tinubu goyon baya

Daily Post ta wallafa cewa wasu kungiyoyi da dama ciki har da wasu gwamnonin adawa sun bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takara.

A wata gagarumar ganawa da aka yi a Abuja watanni hudu da suka wuce,su ma gwamnonin APC da 'yan zartarwar jam'iyyar na kasa da ‘yan majalisa sun amince da Tinubu a 2027.

Haka zalika, a wani taron da tsofaffin ‘yan majalisar tarayya suka gudanar a karshen mako a Abeokuta, jihar Ogun, shugabannin jam’iyya daga shiyyoyin kasar nan sun sake nuna goyon bayansu ga Tinubu.

Sai dai a wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fitar, ya ce APC tana cikin firgici kuma tana neman tursasa mutane su goyi bayan Tinubu.

Kara karanta wannan

An samu bayanai daga majiyar Aso Rock kan takarar Tinubu da Shettima a 2027

APC ta yi martani ga PDP

A martanin da jam’iyyar APC ta yi ta bakin kakakinta na jihar Legas, Seye Oladejo, ta ce PDP ce ke cikin rudani da rikicin cikin gida.

PDP ta ce ana son yi wa 'yan Najeriya dole a 2027
Hoton Shugaban PDP na Kasa, Umar Iliya Damagum Hoto: Umar Damagum
Source: Twitter

Oladejo ya zargi PDP da kasa killace 'ya'yanta da kuma rasa farin jini, yana mai cewa yawan masu sauya sheka daga PDP zuwa APC yana nuna inda karfin siyasa yake a zahiri.

Ya kara da cewa kowanne goyon baya da Tinubu ke samu wata hujja ce da ke nuna cewa 2027 ta APC ce babu ja.

APC ta fara neman gwamnan Ribas

A baya, mun wallafa cewa APC reshen jihar Ribas ta fara shirin jawo ra’ayin Gwamna Siminalayi Fubara domin sauya sheka zuwa jam’iyyar yayin da ake shirin maida shi kujerarsa.

Mai magana da yawun jam’iyyar na jihar Ribas, Darlington Nwauju, ya bayyana cewa jam’iyyar APC a shirye take ta karbi Fubara cikin farin ciki da hannu bibbiyu idan zai dawo cikinta.

Kara karanta wannan

Rikicin NUPENG da Dangote: Kungiyar kiristoci ta fara azumin kwanaki 14

Da aka tambaye shi ko Fubara zai karɓi jagorancin APC a jihar Ribas idan ya sauya sheka, Nwauju ya bayyana cewa hakan zai kasance bisa tsarin jam’iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng