Mutuwa Ta Rikita APC, Mataimakin Shugaban Jam'iyyar Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Mutuwa Ta Rikita APC, Mataimakin Shugaban Jam'iyyar Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Jam’iyyar APC ta shiga jimami a Nasarawa bayan rasuwar jigonta a jihar wanda ya rasu a yau Talata 16 ga watan Satumbar 2025
  • An tabbatar da rasuwar mataimakin shugaban jam'iyyar , Hon. Aliyu Yakubu Barde, wanda ya riga mu gidan gaskiya a Lafia
  • Iyalan mamacin sun bayyana cewa Barde ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, za a yi jana’izarsa a garinsu Wamba bisa tsarin Musulunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - An yi babban rashi a jihar Nasarawa bayan rasuwar jigon jam'iyyar APC mai mulkin jihar da Najeriya.

Majiyoyi sun tabbatar da rasuwar mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Nasarawa, Hon. Aliyu Yakubu Barde.

Mataimakin shugaban APC ya rasu a Nasarawa
Taswirar jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Jam'iyyar APC ta shiga jimami a Nasarawa

Rahoton Leadership ya tabbatar da rasuwar marigayin inda ya ce ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya da ya yi.

Kara karanta wannan

An yi rashi a Kano: Abba Kabir ya kadu bayan rasuwar tsohon sakataren gwamnati

Rasuwar Barde ta jefa jam’iyyar mai mulki a jihar cikin alhini da jimami, inda aka bayyana shi hakan a matsayin babban rashi ga dukan 'ya'yan APC.

Iyalan mamacin sun bayyana cewa, Hon. Barde ya rasu a ranar Talata a birnin Lafia, bayan gajeriyar rashin lafiya da ya yi fama da ita.

An yi rashin mataimakin shugaban APC a Nasarawa
Mataimakin shugaban APC a Nasarawa, Hon. Aliyu Barde. Hoto: Adamu Dogara.
Source: Facebook

Yaushe za a yi jana'izar marigayin?

Majiyoyi sun ce za a yi masa jana’iza a garinsa na Wamba, inda za a yi sallar gawarsa bisa tsarin addinin musulunci kamar yadda aka saba, Daily Post ta ruwaito.

Sakataren APC na jihar, Chif Otaru Douglas, ya tabbatar da mutuwar marigayin ga manema labarai, yana mai cewa rasuwar babban rashi ce ga jam’iyya da al’umma.

Kafin rike mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar, Barde ya taba rike shugabancin kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Wamba a zamanin tsohon gwamnan, Tanko Al-Makura.

Martanin mutane bayan rasuwar Hon. Barde

Shafin Nasarawa Mirror ta tabbatar da mutuwar marigayin inda ta ce ya rasu ne a yau Talata 16 ga watan Satumbar 2025.

Kara karanta wannan

Najeriya ta rasa babban malamin Musulunci, shugaban limaman Ondo ya rasu

Rahoton ya ce da ta wallafa a Facebook ya ce marigayin ya rasu ne kwanaki kadan bayan sallamar shi daga asibitin Lafia a jihar Nasarawa.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu bayan samun labarin rasuwar Hon. Barde bayan fama da jinya na wani lokaci.

Mafi yawan wadanda suka yi martani sun yi masa addu'ar samun rahama inda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki.

Mutari Auwalu Doko:

"Muna rokon Allah ya yi masa rahama ya saka shi gidan aljanna firdausi."

Maryam Isiyaka:

"Innalilahi wa lnna lilahi rajiu Allahu Alkbar, kawu Allah ya maka rahama ya sanya ka gidan aljanna firdausi."

Fitaccen dan kasuwa ya rasu a Nasarawa

Kun ji cewa shahararren ɗan kasuwa kuma dattijon Arewa, Alhaji Isiaku Ibrahim, ya rasu a asibiti a Abuja yana da shekara 88 a duniya.

Ibrahim ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar NPN ta Jamhuriyar biyu, ya kuma kafa Mighty Jets tare da ɗauko koci daga Brazil.

Dan uwansa, Dr. Musa Ibrahim, ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a yi jana’izarsa bayan sallar Azahar a Masallacin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.