2027: Gwamnan Neja, Bago Ya Fadi Abin da zai Tilasta wa Arewa Zaben Tinubu

2027: Gwamnan Neja, Bago Ya Fadi Abin da zai Tilasta wa Arewa Zaben Tinubu

  • Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya bayyana cewa 'yan Arewa sun amince da mulkin Bola Ahmed Tinubu
  • Ya ce yana da yakinin cewa jin dadin mulkin Tinubu a bangarori da dama zai baiwa Tinubu damar koma wa ofis a 2027
  • Umaru Bago ya kara da cewa manyan 'yan siyasar yankin da ke ikirarin babu dan Arewa da zai kuma zaben Tinubu su jira 2031

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana cewa Arewa za ta ba da cikakken goyon baya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen shekarar 2027.

Ya ce yana da yakinin za a yi haka ne saboda Bola Tinubu ya cika dukkanin alkawuran da ya dauka kafin hawa mulki a 2023.

Kara karanta wannan

An samu bayanai daga majiyar Aso Rock kan takarar Tinubu da Shettima a 2027

Gwamnan Neja ya ce Tinubu zai zarce
Hoton Shugaba Bola Tinubu, Mohammed Umaru Bago Hoto: @DOlusegun, @HonBago
Source: Twitter

Gwamna Umaru Bago ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC a ranar Lahadi, inda ya ce Tinubu zai zarce a mulkin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai koma a 2027, cewar Gwamnan Neja

The Nation ta wallafa cewa Gwamnan ya ce yana da yakinin cewa 'yan Najeriya za su yi mamakin irin kuri'ar da Arewa za ta bai wa Tinubu.

Ya ce Tinubu zai ja zugar kuri'a duk da kalaman wasu fitattun 'yan siyasa daga Arewa kamar Nasir El-Rufai da Aminu Tambuwal, da suka ce Arewa ba za ta sake mara wa Shugaban baya ba.

Gwamnan ya ce:

“Na zama Darakta janar na kamfen din Tinubu a 2027, kuma hedikwatar wannan kamfen na nan jihar Neja. Wannan ra'ayi na jama'armu baki daya."

Gwamnan Neja ya goyi bayan mulkin Tinubu

Gwamna Umaru Bago ya ce ya kamata mulki ya ci gaba da kasancewa a Kudu har zuwa 2031, domin tabbatar da adalci, daidaito da zaman lafiya tsakanin Arewa da Kudu.

Kara karanta wannan

Aikin titi: Gwamnatin Tinubu za ta kashe Naira tiriliyan 3 a jihohin Arewa 2

Gwamnan Neja ya ce za a ba wasu yan siyasa kunya
Hoton Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce tsarin mulki na karba-karba a tsakanin Arewa da Kudu ya taimaka wajen rage rikice-rikicen siyasa a Najeriya.

Ya ce:

“A jihar Neja, babu wani sabani. Mun amince da mulkin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu, kuma Tinubu yana shekara ta biyu kacal. Yanzu a ce a dawo da mulki Arewa? Yaya hakan zai yiwu?"

Gwamnan ya ce gwamnatin Tinubu ta bai wa jihohin Arewa damar aiwatar da ayyukan raya kasa, domin ana samun karin kudi daga asusun tarayya fiye da yadda ake samu a baya.

Bago ya bukaci ‘yan Arewa masu burin mulki da su jira har 2031, domin a wancan lokacin ne mulki zai dawo Arewa bisa tsarin da aka amince da shi.

Batun kifar da Tinubu ya fusata APC

A baya, kun samu labarin cewa APC reshen jihar Legas ta mayar da martani mai zafi ga tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, kan kalamansa na cewa Tinubu zai sha kasa a 2027.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya faɗi abin da zai faru da Tinubu da jiga jigan APC da za a watsar

A cewar rahotanni, Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin wani taron ƙaddamar da shirin wayar da kan jama’a da jam’iyyarsa ta ADC ta shirya domin tunkarar zaɓen 2027.

Martanin na APC ya fito ne ta bakin mai magana da yawun jam’iyyar a jihar Legas, Seye Oladejo, wanda ya bayyana kalaman Aregbesola a matsayin marasa tushe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng