An Samu Bayanai daga Majiyar Aso Rock kan Takarar Tinubu da Shettima a 2027
- Wani rahoto ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba ya shirin cire mataimakinsa, Kashim Shettima, daga takarar 2027
- Rade-radin da ke yawo cewa za a nemi sabon mataimaki daga yankin Arewa maso Yamma ya tayar da hayaniya a jam'iyyar APC
- Wata majiya mai tushe daga fadar Aso Rock Villa ta ce a shirye Tinubu da Shettima suke domin yin takara a zaben 2027 mai zuwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – An samu bayanai kan rade-radin da ya bulla a baya cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na duba yiwuwar canza mataimakinsa, Kashim Shettima kafin 2027.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa hakan ba gaskiya ba ne, kuma lokacin zai warware komai.

Source: Facebook
Wani amintaccen mai ruwa da tsaki a Aso Rock Villa ya bayyana wa This Day cewa shugaban kasa bai taba tattaunawa da kowa kan cire Shettima ba.
Lamarin ya jawo muhawarar da ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar APC, musamman daga yankin Arewa maso Gabas inda Shettima ya fito.
An yi rikici a APC kan Shettima a Gombe
A watan Yuni rikici ya tashi a wani taron jam’iyyar APC na Arewa maso Gabas da aka gudanar a jihar Gombe.
A lokacin taron, mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa daga yankin, Mustapha Saliu, ya nuna amincewa da takarar Tinubu karo na biyu, amma bai ambaci sunan Shettima ba.
Wannan ya harzuka wasu daga cikin mahalarta taron, inda aka ruwaito an yi jifa da kujeru da sauran abubuwa, sannan jami’an tsaro suka fitar da Saliu daga dakin taron.
Bayanin Abdullahi Ganduje a wajen taron APC
A wajen taron, tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya maimaita amincewarsa da takarar Tinubu amma shi ma bai ambaci Shettima kai tsaye ba.
Duk da cewa ya yi nuni da cewa shugaban kasa da mataimakinsa tikiti ɗaya ne a tsarin mulki, magoya baya sun ci gaba da rera taken “babu Shettima, babu APC a Arewa maso Gabas.”
Lamarin ya ƙara tayar da kura game da matsayin takarar Shettima da Bola Tinubu a karkashin tikitin APC na 2027.

Source: Facebook
Martanin fadar shugaban kasa kan Shettima
Duk da waɗannan al’amura da suka faru, wani babban jigo a fadar shugaban kasa ya ce babu wani shakku kan matsayin Shettima a 2027.
Rahoton tashar Arise ya nuna cewa ya ce:
“Shugaban kasa zai tsaya da Shettima. Kuna iya rubuta wannan a takarda. Ku daina damuwa da jita-jita, babu gaskiya a ciki.”
Ya ƙara da cewa APC za ta lashe zaben 2027 karkashin tikitin Tinubu da Shettima, yana mai tabbatar da cewa jam’iyyar na da shiri na musamman.
Aregbe ya ce za su kifar da Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa sakataren jam'iyyar ADC ya ce a shirye su ke domin kawar da shugaba Bola Tinubu a 2027.
Jam'iyyar APC mai mulki ta yi martani da cewa maganar kifar da shugaban kasa bata da tushe balle makama.
Kakakin jam'iyyar APC na jihar Legas ne ya bayyana haka, inda ya ce APC ce ta yi wa Rauf Aregbesola komai a siyasa.
Asali: Legit.ng

