APC Ta Kama Tsohon Gwamna Dumu Dumu kan Zargin Taimakon PDP, Ta Faɗi Dalilai
- Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta bayyana yadda ta gano sanata mai ci da ya ci amanarta wanda ya daga mata hankali
- APC ta zargi tsohon gwamna Gbenga Daniel da cin amanar jam’iyya a zaben cike gurbi, inda ya umurci magoya bayansa su goyi bayan PDP
- Duk da wannan mataki, dan takarar APC, Adesola Elegbeji, ya lashe zaben da kuri’u 41,237, ya doke abokin hamayyarsa na PDP da kuri’u 14,324
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Jam'iyyar APC ta nuna damuwa kan cin amanarta da Sanata ya yi a zaben cike gurbi da aka yi.
APC ga zargi Gbenga Daniel na APC daga Ogun ta Gabas da hannu dumu-dumu a zaben yana cin amanar jam’iyya.

Source: Twitter
Shaidar da APC ke da shi kan zargin Daniel
Zaben ya gudana a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025, domin cike gurbin kujerar Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gbenga Daniel, wanda ya taba yin gwamna sau biyu kuma yanzu sanata ne, ana ganin shi a matsayin babban jagoran APC a jihar Ogun.
Sai dai sakonnin WhatsApp da suka bayyana kafin zaben sun nuna cewa Daniel ya umurci magoya bayansa su goyi bayan PDP a maimakon dan takarar APC.
Wani tushe ya shaida wa TheCable cewa, a lokacin yana kasashen waje, amma kuma ya rubuta cewa:
"Ina rokon ku, ku tara dukan mutanenmu da su yi irin zabi da suka yi a baya, zan mara muku baya kamar kullum."

Source: Twitter
Zarge-zargen da ake yi kan Gbenga Daniel
Daga baya ya goge sakon, ya kuma jingina shi da kikkirarriyar fasata (AI) bayan shugabannin APC sun fuskance shi da hujjar wannan matsala da aka gano.
Rahotanni sun ce hakan ba sabon abu ba ne, domin a zaben gwamna na 2023 ma ya goyi bayan PDP a boye, banda tashi.

Kara karanta wannan
Maganar N Power ta dawo, Abba Hikima, Ɗan Bello za su koma kotu da gwamnatin Tinubu
Shugabannin APC sun ce wannan lamari ya zama alamar “cin amanar da ya saba yi” wanda ke nuna rashin kishin jam’iyya daga bangaren sanatan.
Sai dai duk da hakan, wannan umarni bai yi tasiri ba, domin INEC ta bayyana Elegbeji na APC a matsayin wanda ya yi nasara.
Elegbeji ya samu kuri’u 41,237, yayin da abokin hamayyarsa na PDP, Oluwole, ya tashi da kuri’u 14,324 kacal a karshe.
Yadda APC ta dakatar da Gbenga Daniel
Bayan sakamakon, APC ta dakatar da Daniel da mabiyinsa Kunle Folarin saboda zargin ayyukan cin amanar jam’iyya da suka kasa kare kansu a gaban kwamitin.
Jam’iyyar ta ce an aiko musu da gayyata ta rubutu sau da dama, amma sun ki amsa kuma basu bayyana a wurin sauraron shari’a ba.
An yi kokarin tuntubar Daniel don jin ra’ayinsa kan hukuncin, amma kiran waya da sakonni da aka tura masa sun ci tura.
APC ta dakatar da tsohon gwamna
Kun ji cewa jam’iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Gbenga Daniel da wani babban dan siyasa, Hon. Kunle Folarin.
An dakatar da 'yan siyasar biyu ne bayan kin amsa gayyatar kwamitocin ladabtarwa da ke bincikarsu kan zargin cin amanar jam'iyya.
APC ta ce Sanata Daniel da Hon. Folarin sun nuna rashin da'a kuma sun yi yunkurin tursasa wa 'yan kwamitin janye bincike a kansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

