'Za Mu Fitar da Tinubu daga Aso Rock Villa,' Aregbesola Ya Fadi Shirin ADC a 2027
- Sakataren jam’iyyar ADC, Rauf Aregbesola, ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsu za ta hambarar da Shugaba Bola Tinubu a 2027
- Aregbesola ya bayyana cewa ADC za ta kwace Lagos da fadar gwamnati ta Abuja a babban zaɓen 2027 da ke tunkarar kasar
- An kuma samu wata ƙungiya mai suna Conscience Forum daga LP ta koma ADC a lokacin da ta cika shekaru 25 da kafuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Lagos - Sakataren jam’iyyar ADC na kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya ce ADC za ta kwace mulki daga Shugaba Bola Tinubu da kuma jihar Lagos a zaben 2027.
Ya yi wannan furuci ne a wani taro da aka gudanar, inda shugaban ƙungiyar Conscience Forum ta jam'iyyar LP, Hon. Moshood Salvador, ya jagoranci mambobinsa zuwa ADC.

Source: Facebook
An yi taron jam'iyyar ADC a Legas
Taron wanda ya gudana a ranar Asabar, ya kuma kasance bikin zagayowar shekaru 25 da kafa ƙungiyar Conscience Forum a matsayin ƙungiyar siyasa, inji rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mahalarta taron sun hada da shugabannin ADC a Lagos, sakataren ƙasa na jam’iyyar, da shugabannin ƙananan hukumomi 20 da LCDAs 37 (LCDAs) na jihar.
A jawabin sa, Aregbesola ya yaba da shugabanni da mambobin Conscience Forum tare da jaddada musu cewa lokaci ya yi da za su karbi mulki a Abuja da Lagos a 2027.
“Za mu samar da shugaban kasa 2027” – Aregbesola
Aregbesola ya ce:
“Ina farin cikin kasancewa a wannan taro. Ina farin cikin tarbar ku zuwa ADC. Mu ne kawai za mu iya yin wahala ga masu mulki idan Conscience Forum, wadda ta ƙunshi mutane nagari da shugabanci na kirki, ta yi irin wannan taro domin bayyana matsayinta da ADC.

Kara karanta wannan
Sabon tarihi: Dubban 'yan auren jinsi sun gudanar da ziyarar bauta a Vatican a karon farko
“Manufarmu ita ce: mutum ɗaya ya jawo mutane goma, sannan kowannensu ya sake jawo goma. Da zarar mun cimma hakan, sai mu isa fadar gwamnati, kuma za mu samar da shugaban kasa mai zuwa. Saboda haka, mu ci gaba da ƙoƙari, mu canza Najeriya.”

Source: Facebook
Salvador: “LP ba jam’iyyar gaba ba ce”
A nasa jawabin, shugaban Conscience Forum, Hon. Moshood Salvador, ya ce matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar LP sun nuna cewa ba ta da makom, inji rahoton Punch.
“Yau muna bikin zagayowar shekaru 25 da kafa Conscience Forum, kuma lokaci ne da muke kallon abin da muka cimma da kuma inda muka dosa.
"Mun kasance cikin jam'iyyar LP, amma matsalolinta sun nuna cewa ta rasa makoma. Saboda haka, dole mu duba makomarmu a siyasance.
“Mu a Conscience Forum muna da mambobi sama da 400,000 a Lagos. Mun yanke shawarar mu shiga ADC a yau, ranar da muke cika shekara 25."
- Hon. Moshood Salvador.
Aregbesola ya yi bayanin fara aiki a ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya karɓi mukamin sakataren rikon ƙwarya na jam’iyyar hadakar adawa ta ADC.
Rauf Aregbesola ya sha alwashin gina jam’iyya mai ma’ana a siyasa da dogaro da tsari da kishin al’ummar Najeriya.
Tsohon ministan shugaba Muhammadu Buhari ya ce jam’iyyun siyasa ba za su zama wajen cika burin kai wa ga mulki kawai ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

